Maryam Babangida: Matar da ta yi amfani da matsayinta wajen buɗe wa matan karkara sabuwar ƙofa
Daga AISHA ASAS
Mai karatu, barkanmu da sake kasancewa da ku a shafin Gimbiya na jaridarku ta Blueprint Manhaja, shafin da ke waiwayar tarihin mata, nasarorinsu, ƙalubalen da suka fuskanta da kuma gudunmawar da suka bayar wajen sauya rayuwar al’umma.
A wannan makon, za mu waiwayi rayuwar wata jarumar mace da ko bayan shekaru da dama da rasuwarta, har yanzu sunanta yana cikin waɗanda ba za a iya magana kan tarihin mata a Najeriya ba tare da an ambace su ba.
Mace ce wadda rayuwarta ta haɗa aure, iyali, mulki, kwalliya da kuma yunƙurin ganin matan da suka daɗe a bayan fage sun samu damar nuna irin gudunmawar da za su iya bayarwa ga ci gaban al’umma.
Wannan mace ita ce Maryam Babangida, matar tsohon shugaban mulkin soja na Najeriya, Janar Ibrahim Badamasi Babangida, wadda aka fi sani da IBB. Saidai mai karatu ba zan so tunaninka ya tsaya a nan ba, domin idan aka tsaya a nan, za a yi mata kallon matar wani shugaban ƙasa kawai, alhali kuwa akwai abubuwa da dama a tarihin rayuwarta da suka nuna cewa kasancewarta matar shugaban ƙasa ba shi ne kaɗai hanyar da ta sa ta samu matsayi a zukatan mutane ba. Ta yi amfani da damar da ta samu wajen fito da batutuwan da suka shafi mata, musamman waɗanda ke zaune a ƙauyuka, inda mata da dama suke rayuwa cikin ƙalubalen rashin kuɗi, rashin sana’o’i da kuma ƙarancin damar shiga harkokin ci gaban ƙasa.
Abin da ya sa labarin Maryam ya cancanci zama Gimbiyarmu ta wannan mako shi ne yadda ta yi amfani da matsayinta na matar shugaban ƙasa wajen kawo sauyi a yadda ake kallon rawar da mace za ta iya takawa a cikin al’umma. A lokacin da yawancin matan manyan mutane suka fi kasancewa a bayan fage, Maryam ta fito fili, ta yi ɗamar haɗa mata wuri guda, ta kuma kafa wata hanya da ta sa batun ci gaban mata ya zama abin tattaunawa a matakin ƙasa.
Kada in ja ku da nisa, bari mu tsunduma cikin rayuwar gimbiyar ta mu. Shin wace ce wannan mace kafin ta zama uwargidan shugaban ƙasa? Wace irin rayuwa ta yi, kuma me ya sa har yau ake waiwayar sunanta a duk lokacin da aka fara magana kan tarihin mata a Najeriya?
Shin wace ce Maryam Babangida?
An haifi Maryam a ranar 1 ga Nuwamba, 1948, a Asaba, ta Jihar Delta ta yanzu, inda aka raine ta a cikin iyali mai alaƙa da addinai biyu. Sunan da aka haife ta da shi shi ne Maria Ndidi Okogwu, kafin daga baya ta zama Maryam bayan aurenta da Ibrahim Badamasi Babangida. Mahaifinta, Leonard Nwanonye Okogwu, ɗan asalin yankin da ke cikin Jihar Delta ne, yayin da mahaifiyarta, Hajiya Asabe Halima Mohammed, ta fito daga yankin da ke cikin Jihar Neja a yau, kuma Musulma ce. Wannan yanayin iyali ya sa Maryam ta taso a cikin al’umma mai bambancin al’adu da addinai, lamarin da daga baya ya zama wani ɓangare na tarihin rayuwarta.
Ba a san Maryam sosai ba kafin ta auri Babangida, amma hakan ba yana nufin rayuwarta ba ta da nata labarin ba. Ta yi karatu a ƙueen Amina College da ke Kaduna, sannan ta ci gaba da samun wasu horo da suka taimaka mata wajen gina rayuwarta.
Tun a lokacin Maryam ke nuna sha’awa da yunƙurin kawo sauyi a sha’anin tsaftace muhalli, ta kuma nuna ƙwazo a ɓangaren karatu, kula da gida, da kuma kutsa kai a sha’anin da ya shafi ci gaban mata.
Waɗannan abubuwa sun kasance wani ɓangare na rayuwarta tun kafin ta shiga fagen shugabancin jama’a, kuma daga baya suka taka rawa wajen yadda ta gudanar da ayyukanta.
Maryam ta auri Ibrahim Badamasi Babangida a ranar 6 ga Satumba, 1969, a lokacin da yake aikin soja. A wannan lokacin, ba ta zama matar shugaban ƙasa ba, kuma babu wani abu da zai nuna cewa a nan gaba mijinta zai kai matsayin da zai ba ta damar shiga harkokin jama’a a irin wannan fagen da ta shiga. Aure ne da ya fara kamar sauran aure, inda mace da namiji suka fara gina rayuwarsu tare, suna fuskantar ƙalubalen da ke tattare da aikin soja, sauyin wurin zama da kuma kula da iyali.
A cikin littafinsa mai suna ‘A Journey in Service’, wanda ya wallafa a shekarar 2025, Babangida ya bayyana irin rawar da Maryam ta taka a rayuwarsa, inda ya kira ta ginshiƙin tafiyarsa ta rayuwa da aiki. Ya bayyana cewa sun fara sanin juna ne a gidan wani da suka sani, Duba, wanda ke da alaƙa da dangin Maryam. Daga nan ne suka fara kusantar juna, har dangantakarsu ta kai ga aure. A cewarsa, Maryam ta fahimci muhimmancin zaman lafiya a gida da kuma irin gudunmawar da hakan ke bayarwa wajen samun nasara a rayuwar aikin soja.
Wannan bayanin ya nuna wani ɓangare na rayuwar Maryam da ba a cika gani ba idan aka kalli hotunanta na lokacin da take uwargidan shugaban ƙasa. Kafin ta zama mace mai tasiri a harkokin mata, ta kasance mata da uwa, wadda ta yi rayuwa tare da mijinta a lokutan da aikinsa ke buƙatar sauyin wurin zama da kuma jajircewa wajen kula da iyali. Ita da Babangida sun haifi ‘ya’ya, kuma rayuwar iyalinsu ta kasance wani muhimmin ɓangare na tarihin Maryam, duk da cewa daga baya ayyukan jama’a suka sa aka fi saninta a wajen gidansu.
Yaya rayuwa ta kasance wa Maryam daga matar soja zuwa uwargidan shugaban ƙasa?
Aure da aikin soja sun kasance manyan abubuwan da suka tsara farkon rayuwar Maryam. A shekarar 1983, mijinta ya zama babban hafsan sojin ƙasa, kuma daga nan ne ta shiga wani sabon mataki na rayuwarta, inda ta samu damar yin aiki da ƙungiyar matan sojoji. Ta zama shugabar Nigeria Army Officers’ Wives Association (NAOWA), inda ta shiga ayyukan da suka shafi inganta rayuwar matan sojoji da iyalansu. A wannan matsayi, ta taimaka wajen bunƙasa shirye-shiryen da suka shafi horo, sana’o’i, kula da yara da kuma walwalar iyalai.
Wannan aiki ya ba Maryam damar fahimtar matsalolin da mata da dama suke fuskanta, musamman waɗanda suke rayuwa a cikin iyalan da aikin mazajensu ke sa su yawan sauya wurin zama. Ta fahimci cewa mace na da ƙarfin ɗaukar ragamar gida, saidai a lokaci ɗaya tana buƙatar ilimi, sana’a da kuma damar yin amfani da ƙwarewarta wajen taimaka wa kanta da iyalinta, kafin wannan ya tabbata.
Wannan fahimta ce ta zama wani tsani da ta taka, domin sun zama wani ɓangare na manufofin da ta ɗauka lokacin da mijinta ya zama shugaban ƙasa.
A wace shekara mijinta ya karɓi mulki?
A ranar 27 ga Agusta, 1985, Ibrahim Babangida ya karɓi mulkin Najeriya, kuma Maryam ta zama uwargidan shugaban ƙasa. Wannan matsayi ya kawo mata damar shafar rayuka da dama fiye da yadda ta yi a baya, musamman mata.
A lokacin, matsayin uwargidan shugaban ƙasa ba shi da tsarin hukuma da aka tsara kamar yadda ake da shi a wasu ƙasashe, amma Maryam ta yi amfani da matsayinta wajen ƙirƙirar ayyuka da suka shafi mata da yara.
A nan ne labarin Maryam ya fara ɗaukar wani sabon salo. Ta fahimci cewa kasancewarta matar shugaban ƙasa na ba ta damar haɗa mutane, samun kulawar hukumomi da kuma jawo hankalin jama’a kan matsalolin da mata ke fuskanta. Maimakon ta tsaya a kan ayyukan da suka shafi liyafa, tarukan manyan mutane da kuma wakilcin mijinta a wasu bukukuwa, ta fara shirye-shiryen da suka shafi rayuwar mata a ƙauyuka da birane. Wannan ne ya sa matsayinta ya zama sananne a tarihin Najeriya, domin ta haɗa kasancewarta uwargidan shugaban ƙasa da wani shiri na musamman da ya shafi rayuwar mata.
Ko me shirin Better Life da ya sa sunan Maryam ya shiga zukatan mata ya ƙunsa?
A shekarar 1987, Maryam ta ƙaddamar da shirin Better Life for Rural Women, wanda aka fi sani da Better Life Programme. Wannan shiri ya kasance wani yunƙuri na ganin matan karkara sun samu damar inganta rayuwarsu ta hanyar sana’o’i, haɗin gwiwar tattalin arziki, noma, horo da kuma sauran ayyukan da za su taimaka musu wajen samun abin dogaro da kai. A lokacin da mata da dama suke fuskantar matsalolin rashin jari, rashin horo da ƙarancin damar shiga kasuwanci, shirin ya yi ƙoƙarin haɗa su wuri guda domin su samu damar yin aiki tare.
Abin lura a nan shi ne cewa shirin bai tsaya a kan maganganun ƙarfafa wa mata gwiwa ba. An samar da ƙungiyoyin haɗin gwiwar mata, ƙananan masana’antu, gonaki da lambuna, shaguna da kasuwanni, cibiyoyin mata da kuma wasu shirye-shiryen walwala. A wurare daban-daban, mata sun samu damar koyon sana’o’i, haɗa kuɗaɗensu domin gudanar da ayyuka, da kuma samun damar shiga harkokin kasuwanci. Haka kuma, shirin ya yi ƙoƙarin jawo hankalin hukumomi da ƙungiyoyin mata wajen ganin an mayar da matsalolin matan karkara cikin abubuwan da ake tattaunawa a matakin ƙasa.
Idan aka dubi yadda mata da dama suke rayuwa a ƙauyuka, za a fahimci dalilin da ya sa irin wannan shirin ke da matuƙar muhimmanci. Mace na iya yin noma, kula da yara, sarrafa kayan abinci da kuma taimaka wa mijinta wajen neman abin da za a ci, amma duk da wannan gudunmawa, ba lallai ne ta samu damar samun kuɗin kanta ko shiga tsarin yanke shawara ba. Better Life ya yi ƙoƙarin fito da irin wannan gudunmawa, tare da samar da hanyoyin da za su taimaka wa mata wajen inganta rayuwarsu.
Sai dai, kamar sauran shirye-shiryen da suka shafi manufofin gwamnati, Better Life bai rasa masu suka ba. Wasu sun yi tambaya kan yadda ake gudanar da shirin, yadda aka auna tasirinsa da kuma ko dukkan matan da aka tsara taimaka wa sun amfana daidai gwargwado. Waɗannan tambayoyi suna da muhimmanci idan ana son auna nasarar kowane shiri na ci gaban al’umma. Amma a tarihi, ba za a iya musanta cewa Better Life ya sanya batun bunƙasa rayuwar matan karkara a cikin manyan batutuwan da ake tattaunawa a Najeriya ba.
Haka kuma, shirin ya taimaka wajen sauya yadda ake kallon macen karkara. Maimakon a gan ta a matsayin mai aikin gida da noma kawai, an fara ƙara jaddada cewa ita ma mutum ce mai iko da kanta da abin da ta mallaka, wadda za ta iya kafa ƙungiya, ko kasuwanci, kuma ita ma za ta iya bayar da gudunmawa ga ci gaban al’umma.
Wannan ne lamarin da ya kafa tarihin da ya hana sunan Maryam Babangida ɓacewa a tarihin cigaba mata a Najeriya.
Za mu ci gaba a mako mai zuwa.
