
Daga BELLO A. BABAJI a Abuja
Hukumar Zaɓe ta Ƙasa INEC, ta ce za ta gudanar da babban taron ‘yan jarida da masu ruwa da tsaki da duniya a ranar Talata, 6 ga Oktoba, 2026 yayin da ya rage saura kwanaki 100 a gudanar da babban zaɓen 2027 a Nijeriya.
A yayin taron, INEC za ta bayar da ba’asi akan shirye-shiryen zaɓen, ciki har da rajistar masu zaɓe, fitar da sunayen ‘yan takarar, halin mallakar kayayyakin zaɓe da wasu muhimman matakai domin tabbatar da sahihancin zaɓen. Adedayo Oketola, wato Sakataren yaɗa labaran Shugaban INEC, Farfesa Joash Amupitan ne ya bayyana haka a wata takarda da ya fitar a ranar Lahadi, 4 ga Oktoba, 2026.
Ya bayyana cewa, Farfesa Amupitan ne zai jagoranci taron tare da wasu muhimman masu ruwa da tsaki a harkokin zaɓen Nijeriya. Wannan wani ɓangare ne na ƙoƙarin da INEC take yi kan tabbatar da gaskiya da adalci, sanar da jama’a halin da ake ciki a lokacin da ya dace da haɗin-gwiwa da manyan jami’an zaɓe a matakai daban-daban.
Ana tsammanin wannan zama zai haɗa jagororin jam’iyyun siyasa, hukumomin tsaro ƙarƙashin kwamitin shawarwari tsakanin hukumomi kan tsaron zaɓe (ICCES), ‘yan difulomasiyya, abokan hulɗa, ƙungiyoyin al’umma, ƙungiyoyin masu sanya ido, masu kira ga ‘yancin nakasassu, jagororin addini da gargajiya, ƙungiyoyin matasa da jagororin aikin jarida.
Za a gudanar da taron ne a ranar 6 ga Oktoba, 2026 da misalin ƙarfe 10:00 na safe a ɗakin taro na Bola Ahmed Tinubu International Conference Centre (BAT-ICC), wanda aka tsara zai samu halartar waɗanda aka gayyata kaɗai.
Haka kuma, za a haska taron kai-tsaye a gidan talabijin na ƙasa da kuma sahihan shafukan sada zumunta na INEC. Ana kira ga waɗanda aka gayyata daga cikin ‘yan jarida da sauran waɗanda aka gayyata da su tabbatar da gabatar da katin gayyatarsu ko sahihan katinan shaida a shingen binciken jami’an tsaro.
