Daga SANUSI MUHAMMAD a Gusau
Ƙungiyar siyasa ta Kashim Musa Tumsah KMT a Jihar Yobe, ta sake tabbatar da aniyarta na ci gaba da zama a jam’iyyar All Progressives Congress (APC) tare da aiki tuƙuru don ganin an sake zaɓen shugaban ƙasa Bola Ahmed Tinubu da Mataimakin sa Kashim Shettima a zaɓen 2027.
An cimma wannan matsaya ne a cikin wata sanarwa da aka fitar a karshen wani taron da ƙungiyar ta gudanar a Kaduna ranar Asabar, kuma aka rabawa Blueprint Manhaja a Gusau yau Lahadi.
A cewar sanarwar da aka sanya wa hannu a madadin ƙungiyar, mambobi daga sassa daban-daban na Jihar Yobe sun yi cikakken nazari kan halin da siyasa ke ciki da kuma shirye-shiryen zaɓe mai zuwa, domin cimma matsayar ƙungiya da jihar baki ɗaya.
Ƙungiyar ta yanke shawarar binciko hanyoyi daban daban, damammaki da nau’ikan haɗin gwiwar siyasa, yayin da ta tabbatar da cewa za ta ci gaba da zama a cikin APC.
Sanarwar ta jaddada cewa nasara da sake zaɓen shugaban ƙasa Bola Ahmed Tinubu da mataimakin sa Kashim Shettima a zaɓen shugaban ƙasa na 2027 shi ne babban abin da suka tattauna.
Game da takarar gwamnan Jihar Yobe, ƙungiyar ta bayyana cewa ta bai wa dukkan shugabannin ƙungiyoyi daban-daban, a KMT umarnin gudanar da ƙarin shawarwari da mambobinsu da magoya bayansu kan mataki na gaba game da zaɓen gwamna.
Ana sa ran ƙungiyoyin za su miƙa rahotonsu ga sakatariyar ƙungiyar KMT cikin kwanaki bakwai.
Ƙungiyar ta kuma bayyana cewa za ta jira sakamakon ƙararrakin kotu da ke ƙalubalantar zaɓen fidda gwani na APC da bai kammala ba da aka gudanar a Jihar Yobe a watan Mayun 2026.
Ta bayyana cewa muradun Jihar Yobe, magoya bayanta da walwalar al’ummar jihar ne za su kasance ginshiƙin da za a ɗora matsayinta na ƙarshe kan zaɓen gwamna.
Taron na Kaduna ya samu halartar shugabannin ƙungiyoyin goyon baya daban-daban, kuma Barr. Kashim Musa Tumsah, wanda shi ne ɗan takarar gwamna mafi shahara a zaɓen fidda gwani na APC da bai kammala ba a watan Mayun 2026 a Jihar Yobe, ya halarta.
Sanarwar ta ƙara da cewa an umurci shugabannin ƙungiyoyin da su koma yankunan su su sanar da mambobin su cikakken bayani kan matsayar da aka cimma.
