‘Yan majalisar Zamfara takwas sun fice daga APC

Spread the love

Daga SANUSI MUHAMMAD a Gusau

Jam’iyyar All Progressives Congress (APC) a Jihar Zamfara ta fuskanci koma baya mai girma a siyasance bayan da mambobin majalisar dokokin Jihar Zamfara takwas masu ci suka gabatar da takardar murabus daga jam’iyyar a hukumance yau Lahadi.

Ficewar ta jefa ruɗani mai yawa a fagen siyasar jihar, domin biyar daga cikin ‘yan majalisar da suka fice daga mazaɓar Zamfara ta Yamma ne, wato mazaɓar Sanata Abdulaziz Yari, tsohon Gwamnan jihar kuma darakta janar na kwamitin yaƙin neman zaɓen shugaban ƙasa Tinubu 2027.

Ficewar ta biyo bayan ficewar da ta faru mako guda da ya gabata na tsohon ɗan majalisar jiha mai wakiltar ƙaramar hukumar Anka daga 2019 zuwa 2023, Hon. Yusuf Muhammad Anka, wanda ya fice daga APC tare da fiye da rabin shugabannin jam’iyyar a ƙaramar hukumar ta Anka.

Ƙaramar hukumar Anka na cikin mazaɓar Zamfara ta Yamma.

Da yake mayar da martani kan lamarin a cikin wata sanarwa, shugaba kuma jagoran Northwest Youth Unity Forum, Hon. Murtala Ishaka Jangebe, ya ce ci gaba da ficewar manyan jiga-jigan jam’iyyar ta APC a Jihar musamman a Zamfara ta Yamma ya kawo wasiwasi kan ƙarfin Sanata Yari a yankinsa a siyasance.

Mambobin majalisa takwas da suka fice daga APC sune:

Hon. Aliyu Ango Kagara – Talata Mafara ta Kudu, Hon. Ibrahim T. Tukur Bakura – Bakura, Hon. Faruk Musa Dosara – Maradun I, Hon. Barr. Bashir Abubakar Masama – Bukkuyum ta Arewa, Hon. Muktaru Nasiru Kaura – Kaura ta Arewa, Hon. Nasiru Abdullahi – Maru ta Arewa, Hon. Bashar Bello – Bungudu ta Yamma, da Hon. Bashar Aliyu – Gummi

By ukarofi

Leave a Reply