Munafukai a Musulmi

Spread the love


Daga ALI ABUBAKAR SADIK 

Allah ya umarce mu da cewa:
Q49:9 “Kuma idan jama’a biyu ta mũminai suka yi yãki, to, kuyi sulhu, a tsakãninsu. Sai idan ɗayansu ta yi zãlunci a kan gudar, to, sai ku yãƙi wadda ke yin zãlunci har ta kõma, zuwa ga umurnin Allah”
Wannan shine kundin tsarin musulunci. Allah baya son zalunci ba ya son masu zalunci ko a tsakanin misulmi. Don haka idan har zuciyarka ta na jin cewa ka na fatan nasarar Bani Yahudu a kan Iran, to hakika Kai musulmi ne amma ba ka tare da musulunci. Adalci wajibi ne ko a kan kafiri, Allah ya haramta a zalunci kowa don haka duk wanda ya goyi bayan zalunci ba ya tare da Allah. Saboda girman adalci, hatta a kan iyaye, Yaya da mafi kusanci Allah ya wajabta shi
Q4:135 “Yã ku waɗanda suka yi ĩmãni! Ku kasance mãsu tsayuwa da ãdalci, mãsu shaida sabõda Allah, kuma kõ dã a kanku ne kõ kuwa, mahaifa da mafi kusantar zumunta, ko (wanda ake yi wa shaida kõ a kansa) ya kasance mawadãci kõ matalauci, to, Allah ne Mafi cancanta da al’amarinsu. Sabõda haka, kada ku bĩbiyi son zũciya, har ku karkata. Kuma idan kuka karkatar da magana, kõ kuwa kuka kau da kai, to lalle ne Allah Yã kasance Masani ga abin da kuke aikatãwa”
Allah na banbance mũminai da munafikai ta Imani da aiki ba furuci kawai ba. Idan ka na son gane Kai mumini ne ko munafiki to ka Kalli umarnin Allah ka auna da zuciyarka. Idan ka sami nutsuwa a zuciyarka to kai mumini ne, amma idan kuma ka na jin bin wannan umarni ba daidai bane, to shi ma zai baka amsa wanene kai.
Allah ka hade kan musulmai su gane illar da bangaranci da kingiyanci ya haifar mana. Ka bamu ikon bin wannan umarni naka gaba dayanmu
Q3:103 “Kuma ku yi daidami da igiyar Allah gabã ɗaya, kuma kada ku rarraba (kungiyoyi)”
Malam Ali manazarci ne a Kano

By ukarofi