Haɗaka: Zulum ya musanta jita-jitar sauya sheƙa

Spread the love

Daga BELLO A. BABAJI a Abuja

Gwamnan Borno, Farfesa Babagana Umara Zulum, ya yi watsi da jita-jitar da ake yaɗawa a kafafen watsa labarai na cewa zai jagoranci wasu gwamnoni biyar zuwa jam’iyyar haɗakar ƴan adawa ta ADC.

A sanarwar da Kakakinsa, Dauda Iliya ya fitar, Zulum ya bayyana raɗe-raɗin a matsayin ƙaryar da ba ta da asali ko tushe, wadda aka tsirar bisa wata manufa ta siyasa.

Ya kuma jaddada cigaba da biyayya ga jam’iyya mai mulki ta APC a yayin gudanar da harkokin siyasarsa.

Gwamnan, ya kirayi al’ummar jihar da na ƙasa baki ɗaya da su yi watsi da batun, yana mai cewa gwamnatinsa ba ta lokacin siyasanatar da al’amura domin akwai ayyuka da dama a gabanta da ta ke ƙoƙarin aiwatarwa.

Haka kuma, Zulum ya yi kira ga ƴan jarida da su riƙa tabbatar da sahihancin labari tare da ƙaurace wa waɗanda aka ƙirƙira da nufin ruɗar da al’umma.

Kazalika, ya ce za su cigaba da yi wa jihar Borno hidima a ƙarƙashin tutar jam’iyyar APC.

By Babaji