NLC ta yi barazanar shiga yajin aiki bisa ƙamarin talauci da rashin tsaro

Spread the love

Daga BELLO A. BABAJI a Abuja

Ƙungiyar Ƙwadago ta Ƙasa ta yi barazanar tsunduma cikin yajin aiki bisa tsadar rayuwa da rashin tsaro da suka addabi al’umma a Nijeriya.

Ta yi gargaɗin cewa, ma’aikata ba za su cigaba da zura ido ba a yayin da harkar tattali da dimukraɗiyya suke tangal-tangal a ƙasar.

NLC, kamar yadda ta bayyana a taron kwamitin ayyuka a Abeukuta, Jihar Ogun, ta ce halin matsin rayuwar da ma’aikata da talakawa suke fuskanta ya yi tsanani.

Akan haka ne ta kirayi gwamnati da ta gaggauta ɗaukar matakan da suka dace wajen tabbatar da kawo ƙarshen hakan a ƙasa.

By Babaji