Daga MAHDI MUSA MUHAMMAD
Kungiyar Kare Haƙƙin Musulmi ta Nijeriya (MURIC) ta zargi wasu shugabannin Kirista a Nijeriya da fifita muradunsu na ƙashin kansu bayan sun nuna adawa da ƙudirin dokar Hukumar Kiyaye Haɗurra ta Tarayya (FRSC) da ke neman haramta wa’azi da talla a cikin motocin haya.
A cikin wata sanarwa da Daraktan Gudanarwa na ƙungiyar, Farfesa Ishaƙ Akintola, ya fitar a ranar Litinin, MURIC ta bayyana mamakinta kan yadda shugabannin Kirista suka yi watsi da ƙudirin, tana mai cewa manufarsa ita ce rage haɗurran hanya da kuma daƙile rikice-rikicen addini.
ƙungiyar ta bayyana cewa adawar da aka nuna ga ƙudirin ta samo asali ne daga son kai, gajeriyar fahimta da kuma fifita buƙatun wata ƙungiya kaɗai.
Saboda haka ta buƙaci Shugaba Bola Ahmed Tinubu da ya yi watsi da matsin lambar masu adawa da ƙudirin tare da rattaba hannu domin ya zama doka.
MURIC ta ce ƙungiyoyin Kirista biyu ne suka fito fili suna adawa da gyaran dokar FRSC, wato Majalisar Kiristoci ta Nijeriya (CCN) da kuma ƙungiyar Ikklisiyoyin Afirka da Aka Kafa (OAIC).
A cewar MURIC, abin mamaki ne yadda mutane masu ilimi za su yi adawa da wani tsari da aka ce an ƙirƙira domin kare rayukan ‘yan ƙasa da tabbatar da zaman lafiya.
Kungiyar ta yi zargin cewa wa’azi a cikin motocin haya ya zama wata hanya ta neman sababbin mabiya, tana mai cewa shugabannin Kirista sun fi mayar da hankali kan faɗaɗa mabiyansu fiye da kare lafiyar jama’a.
Ta kuma yi kira ga lauyoyin kare haƙƙin ɗan Adam da sauran ‘yan Nijeriya masu kishin ƙasa da su bayyana matsayinsu kan lamarin, tana mai cewa ya kamata a tantance ko wa’azi a cikin mota ya fi muhimmanci fiye da kare rayuka da tabbatar da walwalar fasinjoji.
MURIC ta yi nuni da cewa ƙasashe da dama kamar Amurka, Birtaniya, Faransa da Jamus, ba a yarda da wa’azi a cikin motocin sufuri na jama’a idan hakan na iya haddasa hargitsi ko tayar da hankali.
Ta kuma kawo misalan wasu ‘yan Nijeriya da aka ce an sauke daga motocin haya ko kuma aka kama a birnin Landan saboda yin wa’azi da ya haddasa hargitsi, tana mai cewa dokokin da suka shafi kare zaman lafiyar jama’a sun ba hukumomi damar ɗaukar irin waɗannan matakai.
A cewar ƙungiyar, Nijeriya ma tana da irin waɗannan dokoki, amma babban ƙalubalen shi ne rashin aiwatar da su yadda ya kamata.
MURIC ta ƙara da cewa wuraren ibada sun isa a gudanar da wa’azi, don haka babu wata hujja da za ta sa motocin haya su koma wuraren ibada.
ƙungiyar ta yi zargin cewa wasu shugabannin Kirista na son ƙara yawan mabiya ne domin samun ƙarin kuɗaɗen zakka da gudunmawar mabiyansu, tana mai cewa wannan ne ya sa suke nuna fushi da ƙudirin dokar da ke jiran sahalewar shugaban ƙasa.
Ta kuma yi zargin cewa wa’azi a cikin motocin haya ya zama wata dabara ta yaɗa saƙon addini ga mutanen da ba su da zaɓin kauce wa sauraronsa, saboda yawancin ‘yan Nijeriya na amfani da motocin haya.
A ƙarshe, MURIC ta sake yin kira ga Shugaba Bola Ahmed Tinubu da ya rattaba hannu kan ƙudirin domin ya zama doka, tana mai cewa hakan zai taimaka wajen tabbatar da tsari, kare rayuka da kuma rage rikice-rikicen da ka iya tasowa a cikin motocin sufuri na jama’a.
