
Daga BELLO A. BABAJI
Mutane da dama sun rasa rayukansu a lokacin da wani ƙaramin jirgin sama samfurin jet ya yi hatsari a wata hanyar gidaje dake Birnin California tare da lalata gidaje da ƙonewar motoci.
Kimanin gidaje goma ne suka ƙone da motoci da dama a yankin, wanda ake kira da San Diego.
Hukumar kashe gobara a yankin ta ce suna bincike game da gano adadin mutanen da ke cikin jirgin gami da hakikanin waɗanda suka rasu.
Ta kuma ce, a lokacin da hatsarin ya faru, tankin man jirgin ya fashe tare da tarwatsewa zuwa wurare da dama, lamarin da ya yi sanadin asarar rayuka da dukiyoyin.
