Babu wanda ke juya Tinubu, inji Ministan Labarai

Spread the love

Daga BELLO A. BABAJI

Ministan Labarai da Wayar kan Al’umma, Mohammed Idris ya ce, babu wanda ke juya Shugaba Bola Tinubu a yayin gudanar da harkokin mulkinsa.

A madadin haka Shugaban ƙasar ya kan yi maraba da shawarwari da dama, sannan sai ya yanke hukunci daidai da maslahar Nijeriya.

A sanarwar da mai taimaka masa kan harkar labarai, Rabi’u Ibrahim ya fitar, Ministan ya bayyana hakan ne a Abuja, yayin gabatar da jawabinsa a taron ƙasa na ƴaƴan Jam’iyyar APC da aka yi wa take da ‘Renewed Hope Agenda’, ranar Alhamis.

Ya ce, “Akwai buƙatar ku nazarci Shugaban ƙasar. Za ka iya faɗar ra’ayinka; ka faɗi abinda ka ke son faɗa; zai saurare ka, amma fa yanke hukunci nasa ne kaɗai. Ina ga yana da muhimmanci a gare mu mu fahimci hakan.”

Ya kuma ce, Shugaba Tinubu ya duƙufa ne wajen ciyar da Nijeriya gaba ta hanyar amfani da tsarinsa na Ajandar Sabonta ƙasa, lamarin da ke mayar da kalubale zuwa damanmaki.

Ministan ya ƙara da cewa, tsarin an samar da shi ne kaďai domin inganta rayukan ƴan Nijeriya ta hanyar da ba a taba gani ba a ƙasar.

Har’ilayau, Idris ya bayyana cewa sakamakon gyare-gyaren Tinubu a kowane fanni dalili ne da ke bayyana nasarori, yana mai bada misali da shirye-shiryen zuba jari, inganta ayyukan haķar ma’adanai da ɓangaren albarkatun mai, NELFUND (na tallafa wa karatun daliban manyan makarantu) da sauran su.

Kazalika, a ƙoƙarin tallafa wa ci-gaban tattali na zamani, gwamnati tana aikin samar da wayoyin ‘fiber optic cable’ a faɗin ƙasar da za su mamaye tsawon kilomita 90,000 domin amfanin ƴan Nijeriyar.

By Babaji