
Daga BELLO A. BABAJI a Abuja
Wani tubabben ɗan Boko Haram iƙirarin cewa ya halaka aƙalla mutane sama da guda 100 a lokacin da yake tare da mayaƙan ‘yan ƙungiyar.
Ya bayyana haka ne a wani faifan bidiyo da aka yaɗa ta kafar X, inda tsohon mayaƙin ƙungiyar a yayin ganawa da wani ɗan ƙasar wajen da ya ziyarce su a sansanin gyaran hali tare da wasu tubabbun ‘yan ta’addan.
A faifan, an ga yadda aka samu wani tafinta da ke fassara musu tambayoyin da ɗan ƙasar wajen ke yi musu ta harshen Turanci, inda tubabben ya fallasa cewa ya kashe mutane da dama a daji.
“Na kashe sama da mutane 100”, inji shi.
Ya ƙara da cewa, tun yana ɗan ƙaramin yaro ya shiga ƙungiyar kuma jagororin tafiyar ke sanya shi da ire-irensa shiga munanan ayyuka.
Kazalika, ya bayyana cewa mafi yawancin kisan sun fi aukuwa ne idan suka kai wa ƙauyuka hare-hare, waɗanda a kan ba su umarni wani lokaci su ƙaddamar.
A cewarsa, mata da ake kamawa idan an kai hari, a kan tilasta musu auren mayaƙan a madadin halaka su.
