Maryam Abacha ta kirayi jagororin Arewa su haɗa hannu da Gwamnatin Tarayya wajen magance matsalolin yankin

Spread the love


Uwargidan tsohon shugaban ƙasa, Hajiya Maryam Abacha, ta yi kira ga ƴan Arewacin Nijeriya da su guji zage-zage, tare da tunkarar gwamnati da matsalolinsu domin samar da mafita mai ɗorewa.

Hajiya Maryam Abacha ta bukaci shugabanni, sarakunan gargajiya da ƙungiyoyin matasa na Arewa da su haɗa kai wajen gabatar da ƙorafe-ƙorafensu ga gwamnatin tarayya cikin tsari da mutunci.

Ta ce zagi da cin mutuncin shugabanni ba zai kawo ci gaba ba, sai dai ya ƙara dagula al’amura, tana mai jaddada muhimmancin addu’a da kuma bin hanyoyin da suka dace wajen isar da buƙatun al’umma.

A cikin wata takarda da ta fitar daga birnin Paris na ƙasar Faransa, Hajiya Maryam ta bayyana cewa haɗin kai da tunkarar gwamnati kai tsaye zai taimaka wajen magance matsalolin da suka addabi yankin Arewa, musamman rashin tsaro da talauci.

Ta kuma yi kira ga dukkan ɓangarorin al’umma da suka haɗa da mata, matasa, malamai, attajirai da jami’an tsaro, da su haɗa kai su nemi ganawa da shugaban ƙasa domin tattauna matsalolin yankin.

Hajiya Maryam ta ƙara da cewa yawaitar koke-koke daga ɓangarori daban-daban na iya sa gwamnati ta ɗauki mataki cikin gaggawa, tana mai ba da shawarar a haɗa koke da addu’a domin samun nasara.

Har ila yau, ta yi kira ga masu riƙe da muƙamai a matakai daban-daban na gwamnati da su yi adalci tare da nuna kishin ƙasa a ayyukansu.

Ta kuma nuna takaici kan rashin haɗin kai a tsakanin ƴan Arewa idan aka kwatanta da yadda wasu yankuna ke haɗa kai domin cimma muradunsu.

A ƙarshe, ta bukaci gwamnatin tarayya da ta ƙara mayar da hankali kan matsalolin matasa, musamman rashin aikin yi da matsalar tsaro, domin inganta rayuwar al’umma.

Hajiya Maryam Abacha ta ce ta yi wannan kira ne a matsayinta na uwa ga dukkan ƴan Nijeriya, tare da yi wa ƙasar addu’ar zaman lafiya da kwanciyar hankali.

By Babaji