An yi wa tsohon ɗan takarar sanata ɗaurin shekara 10 kan sayar wa ‘yan ta’adda fetur a Borno

Spread the love

Babbar Kotun Tarayya da ke Abuja ta yanke wa Babagana Habeeb, tsohon ɗan takarar majalisar dattawa a jihar Borno, hukuncin daurin shekaru 10 bisa samunsa da laifin sayar da man fetur ga ‘yan ta’addar Boko Haram.

An yanke hukuncin ne bayan wanda ake tuhumar ya amsa laifin da ake zarginsa da shi na taimakawa ayyukan ta’addanci, inda ya amince cewa ana sayar da man fetur ga ‘yan bindigar da ke aiki a yankin Arewa maso Gabas, ko da yake ya ce ma’aikatan gidansa na mai ne ka iya yin wasu daga cikin cinikin ba tare da saninsa kai tsaye ba.

A yayin shari’ar, lauyan Gwamnatin Tarayya, David Kaswe, ya buƙaci kotu ta tsaurara hukunci zuwa shekaru 20, yana mai cewa irin wannan tallafi ya taimaka wajen kai hare-hare da jawo asarar rayuka da raba jama’a da muhallansu.

Sai dai wanda ake tuhumar ya roƙi sassauci, yana mai bayyana cewa ya shafe sama da shekaru 10 a tsare ba tare da hulɗa da iyalansa ba, tare da nuna cewa yana da mata biyu da ‘ya’ya shida da ke dogaro da shi.

A hukuncinsa, Mai shari’a Peter Lifu ya ce babu wata hujja da ta nuna Habeeb na cikin ƙungiyar Boko Haram ko ya samu horon makamai, yana mai cewa tuhumar ta ta’allaka ne kawai kan sayar da man fetur.

Daga bisani kotun ta yanke masa hukuncin shekaru 10, wanda zai fara aiki daga ranar kama shi, tare da ba da shawarar a yi masa gyaran hali bayan kammala hukuncin.

By Babaji