Mazauna Jigawa sun kama mota maƙare da ababen fashewa

Spread the love

Daga BELLO A. BABAJI a Abuja

Wasu mazauna a yankin Gada da ke kewayen Ƙaramar Hukumar Kazaure a Jihar Jigawa, sun yi nasarar kama wata mota da ake zargin tana ɗauke da kayayyakin ababen fashewa.

Ƙwararre akan harkar tsaro, Zagazola Makama ya bayyana cewa, al’amarin ya faru ne da misalin ƙarfe na daren ranar 10 ga Afrilu, 2026.

A cewar majiyoyi, motar wadda ƙirar Volkswagen Golf ce, an cika ta da kayan boma-bomai, inda wasu ‘yan bijilante suka kama ta.

Majiyoyin sun ce, tuni aka damƙa motar da ababen da aka samu acikinta ga jami’an hukumomin tsaro domin faɗaɗa bincike a kai.

Sun ƙara da cewa, yunƙurin kama waɗanda ake zargi da hannu a jigilar motar ya ci tura sakamakon tserewa da suka yi.

By Babaji