Tsaurin abubuwa ya sa fetur ya yi tsada – Tinubu ga ‘yan Nijeriya

Spread the love

Daga BELLO A. BABAJI a Abuja

Shugaba Bola Tinubu ya bayyana cewa yana sane da halin matsin da al’umma ke cigaba da fuskanta sakamakon hauhawar farashin fetur, yana mai kira ga ‘yan Nijeriya da su cigaba da kasancewa masu kyautata zato da fatan fita daga halin ganin cewa ƙasar tana mataki mai sauƙi akan wasu ƙasashe a game da al’amarin.

Shugaba Tinubu ya yi wannan jawabi ne a jiya Juma’a yayin ziyararsa a jihar Bayelsa, inda ya ƙaddamar da wasu muhimman ayyuka.

Da yake magana akan halin tattalin arziƙi, Tinubu ya ce, “Na saurare ku daga ɓangarori da dama na tattalin. Farashin fetur na matsa lamba, amma idan kuka duba, sai mu gode wa Allah a tare akan gara ku.”

Tinubu ya bayar da misali da wasu ƙasashen Afirka, idna ya ce ƙalubalen da suke fuskanta ba daban ba ne da na Nijeriya, yana mai cewa na ƙasar da sauƙi akan wasu.

Ya ce, gwamnati tana ƙoƙarin ganin ta rage wa ‘yan ƙasa nauyi, sannan ya ɗora wa ƙalubalen harkar tattali a matakin duniya alhaki wanda ya zama sababin shiga matsi a gare su.

Kazalika, shugaban ƙasar ya ce gwamnatinsa tuni ta gabatar da tsare-tsare na rage raɗaɗi da kuma inganta harkokin tattalin arziƙin ƙasa, yana mai bada misali da cire tallafin fetur da ɗaga darajar naira.

By Babaji