Daga ABDULLAHI MUHAMMAD a Katsina
Gwamnatin Jihar Katsina ta ƙaddamar da wani kwamiti na musamman da zai ba da shawara kan yadda za a tsara iyakokin gundumomi cikin adalci, tare da la’akari da tarihi da kuma sauƙin gudanar da harkokin mulki.
An ƙaddamar da kwamitin ne a ofishin sakataren gwamnatin Jihar Katsina, Barr. Abdullahi Garba Faskari, wanda ya jagoranci taron ƙaddamarwar, biyo bayan amincewar Gwamnan Jihar, Malam Dikko Raɗɗa , domin tabbatar da ingantaccen tsari wajen rabon tsofaffi da sababbin gundumomi a faɗin jihar.
Kwamitin zai gudanar da aiki ne bisa jagorancin mai baiwa gwamna shawara kan ayyukan ƙananan hukumomi, Hon. Lawal Rufa’i Safana. A matsayin shugaban kwamitin.
Mambobin kwamitin sun haɗa da wakilan ma’aikatar shari’a,
Wakilan ma’aikatar filaye da tsare-tsare
Wakilan masarautar Katsina da Daura wakilin ma’aikatar yaɗa labarai da al’adu,shugaban ƙaramar hukumar Mani da wakili daga ofishin gwamna.
Aikin kwamitin shine
bai wa gwamnati shawara kan yadda za a tsara iyakokin gundumomi cikin adalci da dacewa sai samar da shawarwari da za su inganta gudanar da sababbin gundumomi da haɗa wasu ƙwararru idan akwai buƙatar taimako.
A nashi jawabin, shugaban kwamitin Hon. Safana ya tabbatar da gudanar da aikin cikin tsari da adalci tare da kammala shi cikin wa’adin da aka ba kwamitin.
Kwamitin zai gudanar da aikin cikin makonni shida domin gabatar da cikakken rahoto kan aikinsa.
