Gwamna Raɗɗa ya gana da jami’an bankin cigaban Musulunci a Katsina

Spread the love

Daga ABDULLAHI MUHAMMAD a Katsina

Gwamnan Jihar Katsina, Malam Dikko Raɗɗa ya gana da tawaga daga bankin musulunci na Islamic Development Bank (ISDB) biyo bayan kammala rangadi na kwanaki biyar kan babban shirin bunƙasa noma a jihar.

Tawagar, wacce Dr. Masuda Saidova ke jagoranta tare da ƙwararru daga hedikwatar bankin daga Jeddah, Saudi Arabia, ta gudanar da ziyartar wurare guda goma sha biyu da aka tanada domin aikin. Wuraren sun haɗa da cibiyoyin noma na Songhai Makera Integrated Agriculture Centre, Garhi Irrigation Scheme, Mairuwa Songhai Centre da Irrigation Scheme, Jachi/Kugado Fadama, Daberam da Gangara Irrigation Schemes, da kuma Tsabu/Sabke Dam, da sauransu.

Aikin da ake shirin aiwatarwa na nufin kafa cibiyoyin noma manya domin ƙara yawan amfanin gona, samar da ayyukan yi, da inganta rayuwar al’umma ta hanyar amfani da tsarin ban ruwa na zamani da dabarun noma masu jure sauyin yanayi.

A taron, Gwamna Raɗɗa ya jaddada aniyar gwamnatinsa na tallafawa wannan shiri, yayin da tawagar ISDB ta yaba da shirin jihar da kuma shirye-shiryenta, tare da bayyana cewa sakamakon wannan ziyara zai taimaka inganta noma, samar da sarrafa amfanin gona a Nijeriya.

By ukarofi