‘Ubangiji ba ya goyon bayan yaƙi’: Paparoma ya gargaɗi Trump akan yaƙar Iran

Spread the love

Daga BELLO A. BABAJI a Abuja

Paparoma Leo na 14 ya yi kira da a kawo ƙarshen yaƙe-yaƙen da ke addabar sassan ƙasashen duniya sakamakon yaƙin da ke gudana tsakanin Amurka da Isra’ila da kuma Iran.

A wata sanarwar da ya fitar ta kafar X, babban limamin addinin Kiristancin ya nesanta addinin daga shiga yaƙin zamani, inda ya ce horo irin na Annabi Isa da koyarwarsa ba su dace da amfani da fin ƙarfi ba wajen muzguna wa wani yanki.

Ya ƙara da cewa, amfani da karfin soja ba zai taɓa kawo zaman lafiya mai ɗorewa ko ‘yanci na gaskiya ba matuƙar ba a dakatar da shi ba, yana mai ankar da jagororin ƙasashen da al’amarin ya shafa.

A cewarsa, tattaunawar sulhu da inganta hanyoyin mutunta juna yayin zamantakewa sune matakan da za su iya janyo samun zaman lafiya mai ɗorewa acikin al’umma.

A ranar 28 ga watan Fabarairu ne Amurka da Isra’ila suka ƙaddamar hare-hare akan Iran, inda suka hari ma’ajiyar makaman nukiliyarta da wasu makamai da kuma shugabancin ƙasar.

Daga nan ne yaƙi ya ɓarke tsakanin ɓangarorin inda Iran ta yi ta mayar da martani akan Isra’ila da sansanonin sojin Amurka da ke yankin Gabas ta Tsakiya.

By Babaji