
Daga BELLO A. BABAJI a Abuja
Ɗan Majalisar Wakilai mai wakiltar Mazaɓar Tarayya ta Dawakin Kudu/Warawa daga Jihar Kano, Muhammad Ɗanjuma Hassan ya rasu bayan shafe shekaru 66 a duniya.
Kakakinsa, Akin Rotimi ya sanar da haka a wata takarda da ya fitar a yau Asabar, inda ya ce ɗan majalisar ya rasu ne a jiya Juma’a, bayan fama da wan irashin lafiya na tsawon lokaci.
Ya bayyana rasuwar a matsayin babban rashi ga majalisar dokokin Nijeriya da ma ƙasa baki ɗaya, yana mai faɗin irin gudunmawar da ya bai wa ci-gaban majalisa na tsawon shekaru.
A cewarsa, tuni Kakakin majalisar Tajudeen Abbas ya miƙa ta’aziyyarsa ga iyalan mamacin, mazaɓarsa da kuma gwamnati da al’ummar Kano bisa babban rashin.
An shirya ya wa marigayin jana’iza a yau Asabar kamar yadda addinin Musulunci ya tanada.
A shekarar 2023 ne aka zaɓe shi a matsayin ɗan Majalisar Wakilai a ƙarƙashin inuwar jam’iyyar NNPP, inda ya yi aiki a matsayin mataimakin shugaban kwamitin majalisar akan harkokin shari’a.
