
Gwamnan Jihar Kano, Abba Kabir Yusuf, ya bayyana cewa tsohon mataimakinsa, Aminu Abdussalam Gwarzo, ya yi yunƙurin cire shi daga mulki domin ya karbi kujerarsa.
Gwamnan ya bayyana hakan ne yayin da ya karbi bakuncin wasu mawaka (Mawallafan Abba Gida Gida) a gidan gwamnati da ke Kano.
Rahotanni sun nuna cewa Gwarzo ya ajiye mukaminsa ne a lokacin da majalisar dokokin jihar ke shirin tsige shi, amma daga baya majalisar ta janye shirin tsige shi bayan murabus din nasa.
Gwamna Yusuf ya ce har yanzu bai ga takardar murabus din tsohon mataimakin nasa ba, yana mai cewa babu wanda ya cutar da shi a gwamnatinsu.
“Yau mataimakin gwamna da muka zo tare a tikiti daya ba ya tare da mu. Babu wanda ya bata masa rai. Har yanzu ban ma ga takardar murabus dinsa ba”, inji gwamnan.
Ya kara da cewa abin da ya sa ya yi hakan shi ne yunkurin karbe masa kujera, amma hakan bai yi nasara ba.
Gwamnan ya kuma yi magana kan masu sukar matakin da ya dauka na ficewa daga jam’iyyar New Nigeria Peoples Party (NNPP), yana mai cewa abubuwan da ke faruwa sun bayyana masu cin amana a siyasa.
Ya ce ficewarsa daga jam’iyyar ba cin amana ba ne, illa matakin kare muradun al’ummar Kano.
A cewarsa, ba a tuntubi ‘yan kungiyar Kwankwasiyya movement ba kafin yanke wasu muhimman hukunci a jam’iyyar, lamarin da ya haifar da damuwa.
Gwamnan ya bayyana cewa bayan ficewar mataimakin gwamna, akwai mutane masu ƙwarewa da dama da ke sha’awar cike gurbinsa.
