Daga MAHDI MUSA MUHAMMAD
Hukumar Kula da Ingancin Abinci da Magunguna ta ƙasa (NAFDAC), a ranar Asabar ɗin da ta gabata, ta kama haramtattun kayayyaki, kayayyakin da suka lalace da kuma waɗanda ba su da rajista da kuɗin su suka haura Naira Biliyan 1.5 a Legas.
Rundunar ‘yan sandan ta NAFDAC ce ta gudanar da aikin a sashen kayan shafawa na kasuwar baje kolin kasuwanci.
Hakazalika, rundunar ta samu nasarar cafke wata tirela ɗauke da jabun kayayyaki.
Dokta Martins Iluyomade, Daraktan Bincike da tabbatarwa, shi ne ya jagoranci tawagar tare da yi wa manema labarai jawabi bayan atisayen.
Ya ce, wannan aiki na daga cikin shirin hukumar NAFDAC na ƙasa na kawar da kayayyaki masu illa a kasuwanni a faɗin ƙasar.
“Mun sami ƙorafe-ƙorafe da yawa daga ‘yan Nijeriya game da kayayyakin da ba su da aminci, kuma wannan atisayen na ci gaba da ƙoƙari kawar da irin waɗannan kayayyaki daga kasuwa.
“Wasu daga cikin kayayyakin da aka kwace sun lalace, kuma kayayyaki ne da aka shigar da su ba bisa ƙa’ida ba, tare da ƙetare hanyoyin gwajin da ake buƙata.
“Mun gano kayayyaki da yawa da suka lalace da har yanzu ana sayar da su a cikin shaguna, adadin ya wuce Naira Biliyan 1.5,” inji shi.
A cewarsa, an gayyaci masu rumbun ajiyar kayayyakin da ba su da kyau domin gudanar da bincike.
“Idan aka same su da laifi, za su fuskanci hukuncin da ya dace na shari’a,” inji shi.
Ya bayyana cewa, NAFDAC, a matsayin hukumar kimiyya, tana amfani da duban gani da ido da gwaje-gwajen ɗakin gwaje-gwaje don tantance amincin samfurin.
“Da farko mun fara gudanar da bincike na gani don tabbatar da ko samfuran sun cika ƙa’idoji.
Ya kuma tabbatarwa da jama’a cewa, NAFDAC za ta ci gaba da yaƙi da jabun kayayyakin da aka haramta, da kuma waɗanda suka lalace.
