‘Yan sanda sun tsare Sowore bisa zargin tunzura al’umma

Spread the love

Daga MAHDI MUSA MUHAMMAD

Rundunar ’Yan Sandan Nijeriya ta tsare ɗan takarar shugaban ƙasa na jam’iyyar AAC a zaɓen 2023 kuma fitaccen ɗan rajin kare haƙƙin bil’adama, Omoyele Sowore bisa zarginsa da yin ayyukan bogi da kuma tunzura jama’a.

An rawaito cewa, a ranar Larabar da ta gabata ne Sashen sanya ido na ‘yan sanda na ƙasa (IGP) ya gayyaci Sowore, wanda ke jagorantar ƙungiyoyin ReɓolutionNow da Take-Back zuwa hedikwatar rundunar da ke Abuja domin amsa tambayoyi. Ya amsa gayyatar da aka yi masa, ya isa harabar da rana tare da rakiyar wasu magoya bayansa.

A cewar wata sanarwa da ƙungiyar ta sa ta fitar, an tsare Sowore ne a ɗaya daga cikin ofisoshin ‘yan sanda da ke babban birnin tarayya, jim kaɗan bayan an yi masa tambayoyi da manyan jami’ai.

Har yanzu dai rundunar ‘yan sandan ba ta bayyana cikakken bayani kan wannan zargi ba, sakamakon binciken da ake yi.

Wata wasika mai ɗauke da kwanan wata ranar Talata kuma aka aika wa lauyan Sowore, Tope Temokun, ta nuna cewa ‘yan sanda su na aiki ne a kan wata ƙara da ake zargin ɗan fafutukar da “tayar da hankali.”

Wasiƙar ta kuma yi nuni da cewa, za a yi ƙarin bayani a yayin ganawar da muƙaddashin Kwamishinan ‘yan sanda (DCP) Akin Fakorede, wanda ke shugabantar sashin sa ido na IGP.

Yayin da yake mayar da martani game da lamarin, Deji Adeyanju, lauya mai kare haaƙin ɗan Adam kuma mai fafutuka, ya yi Allah wadai da tsare Sowore, yana mai bayyana hakan a matsayin rashin amfani da ikon ‘yan sanda.

Ya zargi IGP, Kayode Egbetokun, da tsananta wa Sowore saboda sukar da ya yi kan shugabancin ‘yan sanda, inda ya yi zargin cin hanci da rashawa a hukumar.

Haka zalika, Ana zargin wasu ‘yan sanda daga Sashen Binciken ‘yan sanda na ƙasa sun kutsa inda ake tsare ɗan gwagwarmaya Omoyele Sowore a Abuja, inda suka fita da shi da ƙarfi zuwa wani wuri da har yanzu ba a sani ba.

Haka kuma kamar yadda Sowore ya sanar a shafinsa na sada zumunta na Facebook, ya yi zargin cewa an karya hannunsa yayin da jam’an suka finciko shi da ƙarfin tsiya daga inda yake tsare wajen ƙarfe 6:00 na safiyar ranar Alhamis a ƙoƙarinsu na kai shi kotu ba tare da sanar da lauyansa ba.

Ana kuma son ƙarin bayani kan zargin da Sowore ya yi na cewa, Babban Sufeton na ƙasa ya ƙara wa jami’an ‘yan sandar da ke aiki a gidansa girma ba bisa ƙa’ida ba.

Sai dai ya yi watsi da zarge-zargen inda ya bayyana su a matsayin borin kunya da hukumar ‘yan sandan take don “ɗauke hankalin jama’a daga abin kunyar da Babban Sufeton na ƙasa Kayode Egbetokun da kuma hukumar ‘yan sandan ke aikatawa.

Tuni dai ƙungiyar Kare Haƙƙin Bil’Adama ta Amnesty International ta fitar da sanarwar yin Allah wadai da kamun da hukumar ‘yan sandan ta Nijeriya ta yi wa Sowore wanda ta ce ya sba wa ‘yancinsa na faɗin albakacin baki.

Haka kuma Amnesty International ta buƙaci a saki Omoleye Sowore nan take ba tare da gindaya masa wasu sharaɗi ba.

Shi ma ɗan gwagwarmaya Bello Galadanci da aka fi sani da ɗan Bello, ya yi tir da kamun da aka yi wa Sawore tare da kiran a sake shin an take kamar yadda ya rubuta a shafinsa na Facebook.

By ukarofi