Nagarta: Zulum ya karɓi baƙuncin limamin Ka’aba

Daga AISHA ASAS

Sakamakon nagartar da gwamnan jihar Barno, Farfesa Babagana Umara Zulum ke nunawa a harkar jagorancinsa, ya sanya ɗaya daga cikin limaman Masallacin Ka’aba a Ƙasar Saudiyya, Farfesa Hassan Abdulhamid Bukhari, ya ziyarci gwamnan don yabawa da kuma ƙarfafa masa gwiwa.

Imam Bukhari, wanda babban malami ne a Jami’ar Ummul Qura da ke Makka, ya ziyarci Barno ne a Larabar da ta gabata inda Gwamna Zulum ya karɓi baƙuncinsa a fadar gwamnatin jihar da ke Maiduguri.

Shehun malamin ya yi ziyarar ne bisa gayyatar Dr. Mohammed Kyari Dikwa, wanda shi ne Shugaban Gidauniyar Al-ansar wadda ke kan gina jami’a mai zaman kanta ta farko a Barno.

Yayin ganawarsu da Zulum, Imam Bukhari ya yaba da irin tarbar da suka samu da kuma daɗaɗɗen ilimin Alƙur’ani da aka san jihar da shi. Tare da cewa, Barno ta shahara a duniya ne saboda tarin masana Alƙur’ani da take da su.

Babban baƙon wanda ya yi magana cikin harshen Larabci sannan Dr Dikwa ya fassara zuwa Ingilishi, ya ce ya yi matuƙar jin daɗin mu’amalar gwamnatin Zulum bayan la’akari da irin tarin nasarorin da ya samu.

A nasa ɓangaren, Zulum ya ce akwai daɗaɗɗiyar danganta tsakanin Barno da Saudiyya, musaman ma hadiman masallatan nan biyu masu alfarma. Tare da nuna godiyarsa dangane da ziyarar.

Gwamnan ya ƙara da da cewa, ziyarar ɗaya daga cikin limaman Ka’aba ya zuwa Jihar Barno abin alfahari ga al’ummar jihar, musamman ma musulmi.

Zulum ya yi amfani da wannan dama wajen neman Saudiyya ta taimaka wa jihar Barno a fannin koyar da harshen Larabci da kuma ilimin addinin Islama dai dai sauransu.