Tun ina ƙarama nake da burin zama malamar makaranta – Hauwa Hussaini

Hajiya Hauwa Husaini Muhammad malamar makaranta da takai babban matsayi na shugabar makarantar mata, wato “Principal” kuma ita ce shugabar ƙungiyar yaƙi da cin zarafin mata. A wannan tattaunar da Manhaja ta yi da ita a Kano, za ku ji yadda wannan ƙungiya tata ke fafutuka wajen yaƙi da cin zarafin mata da ƙananan yara wajen ƙwato masu haƙƙinsu musamman a Arewacin Nijeriya.

Daga IBRAHIM HAMISU, a Kano

Zamu so ki gabatar mana da kanki ga masu karatunmu?

Kamar yadda ka sani sunana Hauwa Hussain Muhammad. An haife ni a Kano, na yi karatuna na allo da firamare da sakandare har NCE duka a Kano. Na yi karatun digiri na a fannin nazarin rayuwar ɗan Adam a Jami’ar Ahmadu Bello da ke Zariya.

Ta yaya kika samu kanki a fannin koyarwa?
Aikin koyarwa na faro shi ne tun daga tushe saboda makarantar horon malamai na yi kuma a can na samu shaidar zama malamar makaranta mai daraja ta biyu m, ma’ana ‘grade 2 teacher’ a harshen Ingilishi. Na fara koyarwa tun bayan gama karatuna na Sakandare soboda haka, duk karatun da na yi, na yi shi ne a halin ina aikin koyarwa.

Waɗanne nasarori kika samu a ɓangaren koyarwa?
Nasarata a aikin koyarwa da yawa gaskiya, saboda na fara aikin koyarwa tun daga tushe, ma’ana na fara daga firamare har zuwa makarantar sankandare inda a halin yanzu ina matsayin ‘Principal’ a babbar Makarantar Sakandare ta Mata da ke garin Panshekara. Alhamdulillah. Babban burina tun ina ƙarama bai wuce zama shugabar makaranta ba ga shi kuma burin nawa ya cika, domin a lokacin da nake ƙarama ko wasa ake yi da ‘yan’uwana yara ba ni da wasan da ya wuce na makaranta a soron gidanmu, zan tara yara ina koya masu duk abinda na koyo a makaranta ina yi ina kwaikwayon yanda malamar ta yi mana. Haka kuma daga cikin nasarorin da na samu a harkar koyarwa, shi ne na yaye ɗalibai da dama kawo yanzu ina da ɗalibai da suka kammala karatunsu kuma suna aiki a gurare da dama. Misali a shekarar 2019 na je taron Shugabannin Mayan Makarantun Sakandare a jihar Sakkwato. Wata rana mun fita gurin taro sai buƙatar kuɗi ta kamani na tsaya wani banki zan cire kuɗi a ATM katina ya maƙale, bisa ga mamakina ina shiga bankin dan sanar da su matsalata sai na yi kaciɓis da ɗalibina wanda na koyar nan fa aka nuna mini gata ba kaɗan ba.

Sai kuma a ka ji kin kafa ƙungiya, mene ne sunan ƙungiyar?
Sunan ƙungiya shine
Ƙungiyar Yaki da cin Zarafin Mata da Ƙananan yara.

Mene ne manufofin ƙungiyar?
Manufofin ƙungiyar sun haɗa da:
Kare haƙƙin mata da yara da kuma ƙwato haƙƙin waɗancan mutanen a duk inda ya maƙale.

Ya zuwa yanzu wadanne irin cigaba wannan ƙungiya ta samar ga alumma?
Ƙungiyar mu ta samu ciyar da al’umma gaba musamman abin da ya shafi mata:
Akwai wata da mijinta ya sake ta ɗan taɓu saboda azabar da ya dinga gallaza mata kuma ya rabata da ‘yan’uwanta masu taimakonta, yaranta su ka zama kamar almajirai ba makaranta sai garari suke a gari sakamakon hakan har aka yi wa macen cikinsu fyaɗe, to mun ci nasara mun kai yaran makaranta, ita kuma mun kai ta gun magani ta warke mun ba ta jari. Haka kuma akwai yarinya mai matsalar fyaɗe ita ma ta shiga wani hali sakamakon ƙyama da ake nuna mata. Mun ba ta kumawa, yanzu haka mun samar mata makaranta tana yi kuma mun koya mata sana’ar ɗinki. Sannan akwai yaro da matar ubansa ta nakasa shi a hannu shi ma mun bi haƙƙinsa kuma a halin yanzu karatunsa ya yi nisa har ya shiga babbar sakandare. Akwai irinsu da dama sosai maza da mata.

Waɗanne irin ƙalubale kuke fuskanta a ƙungiyance?
Ƙalubalen da nake fuskasnta bai wuce yanda mutanenmu ke kallon ayyukan ƙungiyarmu da sunan ‘yan baramdan yahudu ba.

Baya ga koyarwa da ya kai ki ga matsayin ‘Principal’ da harkar ƙungiya kina, da wata sa’ana ne ?
Eh ina kiwon kaji masu ƙwai, kuma ina ɗan kasuwanci, ka san Bakano da kasuwa amana ce.

Me kike son cimmawa a rayuwarki?
Babu abinda na fi so cimmawa a rayuwa irin in ga ina taimakon mutane dan ciyar da rayuwarsu gaba musamman mata.

Waɗanne shawarwari gare ki ga al’umma kan bunƙasa ilimi da ƙungiyoyin raya cigaban al’umma?

Shawara ga al’umma bai wuce su tallafa wa karatun ‘ya’ya mata ba, kuma a kula da tarbiyyarsu domin mace ita ce jigon cigaban al’umma baki ɗaya. Ina son mata su sami ingantacciyar rayuwa sosai gaskiya.

Mun gode.
Ni ma na gode Allah ya saka.