Ranar Keke ta Duniya: FRSC ta shawarci ‘yan Nijeriya su koma amfani da kekuna don rage aukuwar haɗurra

Daga UMAR M. GOMBE

Hukumar Kiyaye Haɗurra ta Ƙasa (FRSC) ta ce amfani da kekuna a matsayin hanyar sufuri zai taimaka wajen rage yawan haɗurra da kuma cinkoson abubuwan hawa a hanyoyi.

Shugaban hukumar a jihar Filato, Alphonsus Godwin, shi ne ya bayyana haka a wajen wani gangamin masu tuƙa kekuna da aka shirya a Jos albarkacin Bikin Ranar Keke ta Duniya na 2021.

A cewar jami’in, baya ga rage yawan aukuwar haɗurra, haka nan amfani da keke na taimako wajen inganta lafiya da kuma tabbatar da yanayi mai cike da lafiya, don haka ya shawarci al’ummar Filato da kewaye da su rungumi amfani da kekuna wajen sufuri domin samun amfanin da ke tattare da haka.

Ya ce alfanun da ke tattare da yin amfani da kekuna na da yawa, ciki har da rage cinkoso a kan hanyoyi, rage tsadar rayuwa, taƙaita faruwar haɗurra, a matsayin hanyar motsa jiki da sauransu.

Ya ce, “Ina mai shawartar ‘yan Filato da ma al’ummar Nijeriya baki ɗaya, da su riƙi hawa keke a matsayin hanyar zirga-zirgarsu.” Tare da kira ga jama’a da a zama masu kiyaye dokokin amfani da hanya a kowane lokaci.

A ƙarshe, Godwin ya yi kira ga masu abubuwan hawa da su kula sosai yayin tuƙi musamman ma a wannan lokaci na damina.