Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja
Hukumar Alhazai ta ƙasa (NAHCON), ta bayyana cewa tana nan akan tsarin gaskiya da riƙon amana kamar yadda dokokin da suka kafa ta suka gindaya tare da buɗe kofofinta ga fayyace gaskiya da kuma nesanta daga duk abinda zai tozarta ayyukan hukumar.
Hukumar NAHCON ta fidda sanarwar yin kira ga ‘yan Nijeriya da mutane bakiɗaya da su yi watsi da duk wani rahoto da ke yin cin fuska ga hukumar da zarge-zarge game da yyukan hukumar har sai sun samu tabbacin rahoto daga hukumomin da ke bincike akan duk wata badaƙala da ake zargin an aikata idan har akwai.
Wasu rahotanni da ke yawo a sassa daban-daban na kafafen watsa labarai sun yi iƙirarin cewa hukumar na fuskantar bincike saboda zargin ɓata kuɗaɗen da aka ware don gudanar da aikin Hajji 2025 da ya yi sanadiyyar wasu daga cikin manyan jami’an hukumar ke fuskantar tambayoyi a hukumar EFCC.
A sanarwar da Fatima Usara, Kakakin hukumar kuma mataimakiyar darekta a hukumar, wacce ta sanya hannu a madadin Shugaban/CEO na hukumar a ranar Talata, hukumar ta yi kira da yin roƙo ga jama’a da kafafen yaɗa labarai da su guji yaɗa rahotannin da ba a tabbatar ba tare da barin hukumomin da abin ya shafa su gudanar da aikinsu bisa tsarin doka.
Usara ta kuma jaddada cewa hukumar ba za ta rufe ido ba kan duk wani ma’aikaci ko tsarin da aka samu da laifi.
Hukumar Alhazai ta ƙasa (NAHCON) na sane da wasu rahotannin kafofin watsa labarai da ke yin maganganu kan hukumar, ayyukanta da kuma wasu zarge-zargen da ba a tabbatar ba.
A matsayinta na hukumace da doka ta kafa, NAHCON na ci gaba da gudanar da ayyukanta da cikakken ɗaukar alhakin, gaskiya, riƙon amana da kuma jajircewa wajen samar da ingantaccen aiki. Wannan na cikin aikinta na yi wa mahajjatan Nijeriya da ƙasa baki ɗaya hidima yadda ya kamata.
Hukumar na jaddada cewa, a matsayinta na ƙungiya mai ɗaukar alhakin da ya dace, NAHCON na da alaƙa ta kai tsaye da dukkan hukumomin gwamnati da suka dace, ciki har da na yaƙi da cin hanci da na sa ido. Wannan alaƙa na daga cikin ginshiƙan ayyukan hukumar tare da mutunta tsarin doka da bin ka’ida. Hukumar ba za ta kare ko rufe ido kan duk wani ma’aikaci ko tsari da aka samu da laifi ba.
Sai dai hukumar na kira da girmamawa ga jama’a, musamman kafafen yaɗa labarai, da su yi tauna kalamansu wajen yin hasashe da kuma barin hukumomin da abin ya shafa su kammala aikinsu bisa tsarin doka.
NAHCON ta ce tana mai da hankali kan kimanta, ayyukant musamman bayan aikin Hajji, magance ƙalubalen gudanarwa da kuma ƙarfafa matakan da za su tabbatar da samar da ayyuka da hidima mafi inganci a aikin Hajji ma su zuwa.
