Babu wata zuri’a da ta fi ta sharifai yawa da asali a duniya – Dan Nuhu

Spread the love

Daga MUHAMMADU MUJITABA a Kano

An bayyana cewa babu wata zuri’a a faɗin duniya da take da asali, albarka, daraja da kuma yawa kamar zuri’ar sharifai, “domin ita ce ko’ina ka je a kowace ƙasa za ka samu wanan zuri’a ta Sharifai Ahalullilbati saboda da albarka da asalinta wanda ita zuri’a ce daga Shugaban Halitta wanda shi ne mahaifi ga Saayyada Fatima da mijinta Sayyadi Ali wanda ɗan uwan ne ga Ma’aikin Allah (SAW) su ne asalin Sharifai. kuma shi ne asali mafi tsarki Sayyadi Ali da mai ɗakinsa Sayyada Fatima, ‘yar Manzon Allah, ka ga kenan babu wata zuri’a da ta kai sharifai yawa da asali a duniya,” kamar dai yadda Malam Dannuhu Ismaila ya bayyana a wurin taron nuna farin ciki da zagayowar ranar haihuwar Sayyada Fatima wanda ya gudana a gidan Mumbayya da ke Gwamaja Kano a ƙarshen makon da ya gabata.

Haka kuma ya ce ya wajaba ga dukkanin al’umma da hukomomi wajen girmamawa da kyautatawa Sharifai da ma sauran bayin Allah kamar yadda ya zo a cikin littafin Allah maigirma.

Shi dai Alhaji Ismaila ɗannuhu ya kasance mawaƙin addini ne kuma ɗan kasuwa da ake yi wa laƙabi da Almajirin Malam.

By ukarofi