Naira Miliyan 300 kyauta ce – Martanin NBA ga Kantoman Ribas

Spread the love

Ƙungiyar Lauyoyi ta Najeriya (NBA) ta mayar da martani ga Gwamnatin Jihar Ribas, inda ta bayyana cewa kuɗi Naira miliyan 300 da aka ba su ba su da alaƙa da wani hakkin karɓar baƙuncin babban taron ƙungiyar na shekarar 2025. Shugaban kwamitin shirya taron, Emeka Obegolu, ya ce kuɗin kyauta ne da gwamnati ta bayar ba tare da sharadi ba, kuma ba don samun damar karɓar taron ba ne.

Obegolu ya bayyana cewa NBA na neman tallafi daga hukumomi da ƙungiyoyi daban-daban domin sauƙaƙa nauyin shirya babban taron, amma wannan ba ya nufin cewa gari ko jiha da ta bayar da tallafi za ta samu dama ta karɓi baƙuncin taron kai tsaye. Ya ce babu wata yarjejeniya da ke nuna cewa Fatakwal za ta kasance cibiyar taron saboda bayar da kuɗin tallafi kawai.

A halin yanzu, Gwamnatin Jihar Enugu ta ce tana shirin karɓar baƙuncin lauyoyin Najeriya domin babban taron shekara ta 2025. Shugabar hukumar yawon bude ido ta jihar, Rita Mbah, ta tabbatar da cewa an tanadi sabon ɗakin taro na ƙasa da ƙasa da ke Enugu domin gudanar da taron cikin kwanciyar hankali da jin daɗi. NBA ta sauya wurin taron daga Ribas zuwa Enugu ne bayan rikicin siyasa da ya biyo bayan naɗin sabon shugaban riƙon kwarya a jihar Ribas.

By ukarofi