“Na jima ban samu miji ba saboda suna zargin ina ɗauke da ciwon da ya kashe mijina”
Daga UMAR AKILU MAJERI
Hajia Zainab Garba Fago matashiya ce mai ƙoƙarin neman na kanta domin ta rufa wa kanta da kanta asiri, mace ce mai kamar maza wadda ta jima tana yin gwagwarmaya domin ganin ta rufawa kanta asiri.
Zainab wadda ýar asalin ƙabilar itiloce da ke Jihar Binue a kudancin Nijeriya kuma mahaifiyarta bafillatana ce daga yankin Masarautar Hadejia acan ƙaramar Hukumar Guri. Za mu iya cewa, Hajiya Zainab ruwa biyu ce duk da cewar mahaifinta ɗan ƙabilar Itilone ita kuma mahaifiyarta bafillatana, amma dai bata da wani yare da take yi a matsayin yarenta sai Hausa kuma ta tashi a cikin Musulunci shi ne addininta
Yana daga cikin gwagwarmayar rayuwa da za a ce Zainab ta yi a lokacin da ta yi aurenta na farko a Hadejia, ta auri wani ɗan sanda da ake wa laƙabi da kofur Garba Fago ɗan asalin ƙabilar Cibok da ke Jihar barno.
Aurensu ya yi albarka, sun sami ƙaruwa da yara biyu Hannatu da daddy dukkansu suna raye a hannunta kuma suna rayuwa irin ta hausawa Musulmi.
Zainab ta samu sauyin rayuwa a lokacin da mijinta kofur Garba Fago ya kamu da jinyar ajali da kuma lokacin da ya bar duniya ya koma ga mahaliccinsa. Yan uwansa sun yi iyakacin ƙoƙarinsu na su raba ta da yaranta, amma ba su sanu nasara ba saboda ta tsaya da ƙafarta wajan kula da ‘ya’yanta.
Sakamakon haka ne Hajiya Zainab Garba Fago ta tashi tsaye wajan yin sana’a domin kula da ‘ya’yanta na abinda ya shafi makarantarsu da lafiyarsu da kuma abinda zasu ci abakinsu.
Wakilinmu na Jihar Jigawa Dutse, Malam Umar Akilu Majeri, ya samu damar zantawa da Hajiya Zainab Garba a gidan sabon mijinta da ke unguwar Rajo a Jihar Jigawa a garin Dutse fadar gwamnatin Jihar Jigawa. Ya kuma fara da yi mata tambaya kamar haka;
MANHAJA: Yaya sunanki ?
ZAINAB FAGO: Sunana Zainab Garba Fago, amma yanzu sunana Zainab Umar Danladi.
Zan so na san tarihinki?
An haife ni a Hadejia a unguwar Gandun Sarki a shekarar 1996. Mahaifina ɗan sanda ne a barikin yansanda na Hadejia anan muka zauna anacemar Sajan ɗanladi kuma mahaifiyata bafillatana ce daga ƙaramar Hukumar Guri, mahaifina ɗan asalin Jihar Binue ne daga ƙabilar Itilo muna da alaƙa da tiɓi, wato kabilar tibi.
Mahaifiyata tanacemin Baturiya saboda ni fara ce ƙar kamar Baturiyar Amurka, kuma mahaifinmu ya haife mu a Hadejia da Babura. Ni da Usman yayana da kanina Dauda, da Audu, da kanwata Ummi wadda ni ce ta biyu a bayan babban wanmu Usman.
Bayan na gama sakandire a Malam Maɗori anyi min aure na auri ɗan sanda kasancewar na taso a cikin barikin yansanda na Hadejia shi ne na auri kofural Garba Fago.
Mijina Garba Fago yana sona ina sanshi ni a rayuwata bansan wani abu kishi ba sai bayan mutuwar mijina Garba Fago da na yi sabon aure bayan mutuwarsa domin aure muka yi irin na turawa ‘one man one wife’ badan mutuwa ba da har yanzu muna tare.
Wacce irin jinya ce ta yi sanadin mutuwar mikinki?
Ya yi fama da ciwon hanta domin takai ta kawo yana yin aman jini kafin ya mutu. Da ya mutu na jima ban yi aure ba, saboda maza suna zargin ko ina ɗauke da ciwon saboda shi ciwon hanta ana ɗaukarsa, amma ni Allah ya kare ni ban ɗauka ba domin ana ɗauka, amma ba wai masu so na rasa ba ina da masoya na kai shekaru shida ina zaune a gida ina nazari Ina addu’a Allah ya kawomin miji nagari. Shi ne Allah ya haɗa ni da wannan mijin nawa.
Yaya aka yi kika aure shi, wato shi mijinki na yanzu?
To ni dai ban san shi ba, shi ma bai sanni ba. Mun je Dutse ni da wasu mutanen Kafin Hausa da suke taimakamin wajan neman haƙƙin mijina a sakateriyar gwamnatin Jihar Jigawa ofishin saɓacom inda ake bin hakkin yansanda da sauran ma’aikatan gwamnatin tarayya, to a nan ya ganni muka yi magana shine yazo gidanmu a Hadejia daga nan Allah ya ƙulla aurenmu.
Anan ne ya ganni ya yi wa abokan tafiya ta magana ya ce, yana sona, ya bada lambar wayarsa ya ce, inna amince na kira shi mu yi magana. Da yake Allah ya ƙulla abin, yau ya’yanmu biyu tare da shi kuma ya sani akan hanyar da zan iya dogaro da ita koda ace yau ba ya duniya ina yin alfahari da rayuwata da shi.
Bayan rasuwar mijinki wacca rayuwa kuka yi ?
Bayan rasuwar mijina na ga sauyi sosai, kasancewar ban san wata sana’a ba sai dai na yi wanka na yi kwalliya na zauna kujera ina jirashi ya dawo. Amma bayan mutuwarsa ni ce kitso, ni ce ɗanwaken sayarwa, koyan ɗinki har koko da kosai na yi na sayarwa domin na rufa wa kaina asiri da yarana.
Bayan na yi aure anan Dutse da sabon mijina ya riƙa sayo min itace ina sayarwa, yana sayo min gawayi ina sayarwa domin na kasance wadda zata dogara da kanta. Mijina bai tsaya nan ba ya saka ni makarantar koyon ɗinki na zamani, a yanzu haka ina cikin koyo kuma ina ganin alfanon ɗinkin.
Wato dai rashin sana’a ga mata na da illa kenan?
Gaskiya rashin sana’ar mace yana da illah yayin zaman aure, duk matar da ta dogara da miji ta ƙi yin sana’a, idan mijinta ya riga ta mutuwa zata sha mamaki matuƙar bata iya sana’a ba.
Domin sau da yawa mace idan ta damu kanta a irin halin da na samu kaina in bata da iyaye na gari kuma bata da wata madogara takan faɗa wata sabuwar rayuwa da ba ta taɓa yi ba abaya domin ta samu madogara in bata samu biyan buƙata ba, zata iya faɗawa halaka.
Amma ni na gode Allah ban taɓa shiga wata mummunar rayuwa ba kuma duk mutumin da ya zo guna idan ya duba yaga babu fuska awajena ba ya sake dawowa domin bai ga fuskar wasa ba. Iyayenta talakawa ne, amma sun bani tarbiyya ta addinin Musulunci, ba na zina kuma ba na san miji mazinaci, shi ya sa har kullum addu’ata Allah kada ya ban miji mazinaci, kuma Allah ya amshi addu’ata domin na yi Imani mijina ba ya yin zina. Na gode wa Allah.
Menene shawararki ga ‘yan uwanki mata?
Shawarata ga mata kada su dogara ga mazajensu, su tsaya su koyi sana’a domin ba s san gawar fari ba, domin yanzu ankai wani zamani da ‘yan uwa ba sa iya kula da ‘ya’yan ‘yan uwansu a lokacin da suka bar duniya, sai dai a rungumi yara domin a kwashe dukiyar ubansu, a bar uwarsu da wahala, shi ya sa ya zama dole mata su tashi tsaye su koyi sana’a, domin su bai wa ‘ya’yansu kulawa a lokacin da suke buƙatar kulawar mahaifinsu bayan mutuwarsa.
Amma idan mace tana da sana’a to tana da madogara wadda za ta iya kula da yaranta koda za ta samu matsala zs ta zo mata da sauƙi.
Wane abu ne ya fi burge ki?
Abinda ya fi burge ni, mijina na yanzu, yana burge ni yana yi min abinda bakowane namiji zai yiwa mace ba. Ya riƙe min ‘ya’yana tamkar shi ne ya haife su, yana ba su kulawa babu bambanci da ‘ya’yan cikinsa kuma ya gaya wa ‘ya”yansa cewa ni fa ýar uwarsa ce auren zumunci muka yi ya sa kowa daga cikin ‘ya’yansa suna ba ni daraja ni kuma na riƙe ‘ya’yansa tamkar ni ce na haife su.
Shi ne yake kula da karatunsu ya sanya su a makaranta mai tsada yana kula da lafiyarsu tamkar babansu ba shi da kyashi, ba ya ganin laifina yana sona kamar zai haɗiye ni, ba ya san yaga bacin raina haka uana burge ni sosai.
Ance kina da kishi. Me ya sa kike kishin mijinki?
Ina kishinsa saboda yana ba ni kulawar da ya kamata, domin ban taɓa samun kulawa ba tun da na yi aure sai da na aure shi. Na ga sauyi a rayuwata yanzu kamar a gunsa ma na fara yin rayuwa domin wata sabuwar rayuwa nake yi da shi saboda kulawar da nake damu awajansa. Mijina mutum ne mai kwazo, gwarzo ne kuma sadauki a cikin mazaje. Mata ‘yan uwana sun gane abinda nake nufi. A cikin maza samun irinsa yana da wahala, sai an tona. Shi ya sa nake kishinsa bana san na ji ya ce, zai yi aure ko kuma ace min wai zai yi aure domin tunanina kada wata ta raba ni da shi domin yana sona ina san shi.
Za mu so jin ko ya yi maki kishiya ko kuwa haryanzu?
Ya yi aure, amma har yanzu muna tare domin ns gaya ma muna san juna mun zama tamkar cingum.
Malama Zainab Na gode.
Ni ma na gode.
