
Daga BELLO A. BABAJI
Jami’an Sojoji na runduna ta 3 ƙarƙashin Atisayen SAFE HEAVEN (OPSH), sun yi nasarar ceto mutane 16 da aka yi garkuwa da su akan hanyar Jos zuwa Mangu a Jihar Filato.
Kakakin Atisayen, Manjo Samson Nantip Zhakom ya bayyana hakan a wata takarda, ranar Litinin.
Ya ce, jami’an Atisayen LAFIYAN JAMA’A ne suka gano wata mota a gefen hanya ba tare kowa aciki ba, a yankin Mararaban Kantoma dake Mangu da misalin ƙarfe 9 na dare.
Lamarin da ya sa suka bazama dazukan da ke kusa don nemo waɗanda ke cikin motar.
Ganin jami’an suna tunkarar wajen da suke ya sa ƴan bindigar suka buɗe wa sojoji wuta, sai dai ƙarfin makaman sojojin ya fi nasu yawa a yayin da aka fafata. Lamarin da ya sa suka gudu tare da barin waɗanda suka yi garkuwa da su a wajen.
Ya kuma ce, sun yi nasarar ceto mutane 16 waɗanda daga ciki akwai ƙananan yara shida.
Kazalika, dakarun sun yi ƙoƙarin bada agajin gaggawa ga waɗanda suka samu raunuka a yayin aukuwar lamarin.
Har’ilayau, sojojin sun kai mutanen cikin garin Jos don cigaba da gudanar da sufurinsu, yayin da kuma suka bazama binciken ƴan bindigar da suka tsere bayan sun samu raunuka.
