Mataimakin shugaban ƙasa Sanata Kashim Shettima ya isa Jihar Akwa Ibom,
domin ƙaddamar da shirin tsare-tsaren cigaban al’umma na ARISE,wanda za a aiwatar a ɗaukacin ƙananan hukumomi.
A wani ɓangare na fatan shugaban ƙasa Bola Ahmad Tinibu na samar da cigaba ga al’ummar Nijeriya,wanda ke da nufin inganta ƙwarewar ma’aikata har ma da inganta tattalin arziki.
A yayin isowar sa, Sanata Kashim Shettima, ya samu tarba daga Gwamnan Jihar Akwa Ibom, Fasto Dr Umo Eno da sauran jami’an gwamnatin jihar.
Shettima, wanda shine shugaban majalisar tattalin arziki na ƙasa (NEC) da kwamitin shirye-shirye kan cigaban al’ummar Nijeriya, zai ƙaddamar da ayyuka da dama ƙarƙashin shirin na ARISE, ciki har da inganta cibiyoyin kiwon lafiya matakin farko, inganta ilimin makarantun firamare, haɗi da samar da cibiyoyin jin ƙai da cibiyar koyon sana’o’i, da kuma inganta ɓangaren muhalli.
