Daga ABDULLAHI MUHAMMAD a Katsina
Watanni kusan uku da suka wuce aka gudanar da zaɓen ƙananan hukumomi inda jam’iyyar APC da ke kan mulki ta lashe duka kujerun shugabannin ƙananan hukumomi 34 da na kansiloli a jihar.
Sai dai jam’iyyar adawa ta PDP bata shiga zaɓen ba sakamakon rikicin cikin gida da ya ta dabaibaye jam’iyyar.
Shugaban jam’iyyar APC na ƙasa Dr Abdullahi Ganduje na ɗaya daga cikin waɗanda suka halarci bikin rantsuwan da ya gudana a filin wasa na Muhammadu Dikko a Katsina.
Da yake jawabi gwamna Dikko Raɗɗa ya bayyana cewa jam’iyyar APC a jihar ta bi duk ƙa’idojin da uwar jam’iyyar ta ƙasa da hukumar zaɓe suka tanada kan zaɓen ƙananan hukumomi.
Ya gargadi zaɓaɓɓun shugabannin ƙananan hukumomin da su rinƙa zama a ƙananan hukumomin su domin su ji koke koken al’ummar su.
Raɗɗa ya ƙara da cewa zai naɗa mai ba shi shawara akan ƙananan hukumomi domin kyautata dangantakar su da gwamnati.
Haka kuma yayi kira ga kowane ɗan majalisar dokoki da ya rinƙa sa ido a ƙaramar hukumar sa domin tabbatar da ganin shugabannin sun gudanar da aikin raya ƙasa a yankunan su.
Gwamnan ya bayyana cewa wannan shine karo na farko da zaɓaɓɓun shugabannin ƙananan hukumomi a jihar zasu miƙa ragamar mulki ga wasu zaɓaɓɓun shugabannin.
Ya shawarci shugabannin da su mai da hankali akan harkar ilimi, kiwon lafiya da cigaban matasa .
“Ina tabbatar maku da haɗin kan gwamnati da taimakawa wajen samar da ababen more rayuwa a ƙananan hukumomin ku”Dikko Raɗɗa yace.
