Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja
Gwamna Dauda Lawal na jihar Zamfara ya ce Naira miliyan 4 kawai ya tarar a baitul malin jihar lokacin da ya karɓi mulki.
Dauda Lawal ya bayyana haka ne a wata hira da aka yi da shi a gidan talabijin na Channels Tɓ mai taken siyasa a yau.
Ya ce ya ƙara kuɗin shigar jihar daga naira miliyan 90 zuwa naira biliyan 2 a kowane wata.
Lawal ya ƙara da cewa abubuwa ba sa tafiya dai-dai a lokacin da ya karɓi ragamar mulki, inda ya ce an bar ɗaliban jihar a halin rashin tabbas saboda ba za su iya zana WAEC da NECO na tsawon shekaru biyu ba.
Ya ce, “lokacin da na karɓi mulki, abin da na tarar da shi a baitul malin Jihar Zamfara Naira miliyan 4 ne kacal, abin da na samu ke nan. Akwai shaidu da takardu da suka nuna hakan.
“Daga baya na yi tunani cewa ai shugabanci ne. Sai na fara tunanin mafita.
“Idan muka dawo kan IGR, lokacin da na karbi ragamar mulki, IGR a jihar Zamfara Naira miliyan 90 ne kacal, ka yi tunanin me? Kashi 90 na wannan Naira miliyan 90 ne ake biya, amma labarin ya canza yanzu, zan iya cewa a yanzu muna samun sama da Naira biliyan biyu a kowane wata,” inji shi.
