Gwamnatin Katsina ta kashe biliyan N150 wajen gina hanyoyin kilomita 160

Spread the love

Daga ABDULLAHI MUHAMMAD a Katsina 

Gwamnatin Katsina ta kashe Naira biliyan 150 wajen gina hanyoyi na tsawon kilomita 160 a jihar.

Kwamishinan ayyuka da gidaje, Injiniya Dr Sani Magaji ya faɗi haka a hira da manema labarai a ofishinsa.

Ya bayyana cewa a cikin wannan aiki akwai manyan tagwayen hanyoyi masu tsowon kilomita 55.7 da za su ci kuɗi Naira biliyan 74.95.

Injiniya Magaji ya sanar da cewa wasu a ciki hanyoyin an kammala su kamar babban tsagin hanyar da ta taso daga Jami’ar Umar Musa Yar’Adua ta ƙare a ‘yan ɗaki da Shugaban ƙasa Bola Tinubu ya buɗe a ziyarar aiki da ya kai jihar kwanan baya.

A cewarsa shi wannan tagwayen hanya mai tsawon kilomita 24 an samar da fitila mai haske rana a hanyar.

Akwai hanyar da ta taso daga ƙofar gidan Sarkin Katsina wato ƙofar Soro zuwa ƙofar da shi ma an kammala.

Kwamishinan ya bayyana cewa wasu aikin ya kai gaɓan kammala wa wasu kuma an yi nisa da aikin.

Aikin hanyar da ta tashi daga babban masallacin Juma’a na ƙofar Soro zuwa ƙofar Marusa ya kai har zuwa WTC za a kammala cikin wannan wata kuma ana sa ran gwamna Dikko Raɗɗa zai buɗe ta.

Injiniya Magaji ya tabbatar da cewa za a kammala ayyukan hanyoyi da gwamnatin Dikko Raɗɗa ta bada kafin wa’adin mulkin wannan gwamnati ya ƙare.

Ya ce wannan gwamnati ta gaji bashin fiye Naira biliyan 6 da tsohuwar gwamnatin Masari bata biya ‘yan kwangilar da suka fara aikin wasu hanyoyi a jihar.

“Amma saboda muna so a cigaba da aikin hanyoyin da ba a kammala muka biya ‘yan kwangilar Naira biliyan 7 duba da tashin farashin kayayyakin aikin hanyar,” Dr Magaji ya ce.

Ta ɓangaren gidaje kuwa kwamishinan ya sanar da cewa gwamnatin jihar na nan na tattaunawa da wani bankin bada lamuni a ƙasar domin gina gidaje guda 500 a kowace shekara.

Ya ce gwamnati za ta nemo masu zuba hannun jari kan harkar gidaje domin shiga cikin shirin.

By ukarofi