Malami ya ja kunnen magoya bayansa

Spread the love

Daga JAMIL GULMA a Kebbi 

Tsohon Antoni Janar kuma ministan Shari’a Abubakar Chika Malami ya ja kunnen ‘yan siyasa musamman magoya bayansa da su kauce wa duk wani abu da zai kawo rarrabuwar kai da tashin hankali a cikin al’umma. 

Wannan bayanin yana ƙunshe ne a wani rubutu da Mohammed Bello Doka, mai taimaka masa ta hanyar yaɗa labarai ya aike ta shafinsa na yanar gizo farkon makon nan.

Takardar ta bayyana cewa siyasar ƙwarai ba ta da alaƙa da cin zarafi ko zage-zagen juna saboda aikata haka ba abinda ya ke haifarwa illa tarwatsa mutane.

Saboda haka duk wanda ke neman jama’a ba shi ne ya kamata ya fito yana zage-zage da cin mutuncin mutane ba, abinda siyasa ta gada shi ne sulhu da haɗa kan al’umma saboda haka ministan na shari’a ya nemi magoya bayansa da su cigaba da yaɗa manufofinsa da abubuwan da ya kawo na ci gaba.

By ukarofi