Daga ABDULLAHI MUHAMMAD a Katsina
Gwamnatin Jihar Katsina ta amince da bada Naira miliyan 99 don gyara filin wasan ƙwallon ƙafa na garin Funtuwa.
Kwamishinan wasanni Aliyu Zakari Shargalle ya sanar da haka a garin Funtua lokacin da yake miƙa takardar kwantaragin ga ɗan kwangilan.
Ya sanar da cewa Gwamna Dikko Raɗɗa ne ya bada kwangilar aikin ganin yadda filin wasan ke da muhimmanci wajen haɓaka wasanni a jihar.
Aliyu Zakari ya bayyana cewa ayyukan da za a yi a filin wasan ya haɗa da gina magudanan ruwa, katangar filin wasan da waya da sanya ciyawa irin wanda ake sawa a manyan filayen ƙwallo a duniya da shata wurin guje-guje da tsalle.
Ya ce ana sa ran kammala aikin cikin watannin huɗu masu zuwa.
Da yake maida martani ɗan kwangilan Injiniya Abu Kasim ya tabbatar wa kwamishinan cewa za su gudanar da aikin filin wasan da zai zama ɗaya daga cikin manyan filayen wasa na duniya.
Ya kuma yi alƙawarin kammala aikin kamar yadda aka yi yarjejeniya da kamfaninsa.
Injiniya Kasim ya yi godiya ga ga Gwamna Dikko Raɗɗa da yaga dacewar kamfaninsa na gudanar da aikin.
Filin wasan da aka sa masa sunan Marigayi Sama’ila Isa Funtua da ya ƙumashi wajan wasan ƙwallon ƙafa, ƙwallon hannu, ƙwallon kwando da na gujeguje da tsalle-tsalle amma gaba ɗaya filin ya koma wajen noma saboda ba a amfani da wurin.
