
Daga BELLO A. BABAJI
Mai bai wa shugaban ƙasa Shawara kan Harkar Tsaro, Malam Nuhu Ribaɗu, ya ce gwamnatin shugaba Bola Tinubu za ta tabbatar da kawo ƙarshen sabuwar kungiyar ƴan ta’adda ta Lakurawa a shiyyar Arewa-maso-Yamma nan ba da jimawa ba.
Ribaɗu ya bayyana haka ne a lokacin da ya wakilci Shugaba Tinubu a wajen bikin babban taron Hukumar Kwastom na shekarar 2024 a ranar Laraba, a Abuja.
Ribaɗu ya ce, “Za mu fatattaki waɗanda ake kira Lakurawa daga ƙasarmu. Za mu kunyata masu sukar mu kuma zamu rufe bakunansu. Boko Haram da suka addabi ƙasarmu a baya, yanzu tserewa suke. Yanzu haka mambobinta suna tafiya zuwa wasu ƙasashe makwaɓta saboda basu da damar yin ta’addancin su a Nijeriya.”
Ya kuma ce, alamu na ƙara nuna cewa al’amura na cigana da inganta ta fuskar tattalin arziƙi a ƙasar nan wanda kowa zai iya gani, inda ya bada misali da yadda ake haƙo ɗanyen mai a yankin Neja-Delta da kuma sauye-sauyen kasafin kuɗi da babban bankin Nijeriya (CBN) ke yi a cikin irin wannan ƙoƙari.
“Haƙar ɗanyen mai ya kai ganga miliyan 1.8 a kowace rana. Sannan kuma an tsaftace babban bankin ƙasa; babu wanda ke ɗaukar kwabo daga babban bankin. Mun yi alƙawarin cewa za mu gyara ƙasar nan, kuma za mu yi hakan domin Shugaba Tinubu bai taba zama mutum mai gazawa ba”, inji Ribaɗu.
