Da Ɗumi-Ɗumi: Wata tankar mai ta ƙara fashewa a Jigawa

Spread the love

Wata tankar mai ɗauke da man fetur ta kama da wuta a kan iyakar Jigawa da Kano, lamarin da ya jefa tsoro a zukatan mutanen da ke wajen. Jami’in hulɗa da jama’a na hukumar kashe gobara ta tarayya a Jihar Jigawa, Aliyu M. A ya tabbatar da faruwar wannan lamari ga manema labarai a ranar Laraba, 13 ga watan Nuwamba, 2024.

A cewar Aliyu, “A ranar 12 ga watan Nuwamba, 2024, da misalin ƙarfe 10:43 na safe, hukumar kashe gobara ta samu kiran gaggawa daga dagacin Kuho, Zubairu Ahmad, kan hatsarin tankar da ya faru a Tsaida, Kwanar Kalle, kusa da ƙauyen Gamoji a kan titin Maiduguri.” Ya ƙara da cewa, “Jami’an FFS sun isa wurin cikin ƙanƙanin lokaci da misalin ƙarfe 10:50 na safe, inda suka yi nasarar shawo kan wutar.”

Wannan al’amari ya faru ne wata ɗaya bayan makamancin irin wannan lamarin a watan Oktoba wanda ya yi sanadiyar rasuwar sama da mutane 170. Tankar mai ɗauke da man fetur ɗin wanda ke tafiya daga Kano zuwa Nguru a Jihar Yobe, ta yi bindiga a Majia da ke Ƙaramar hukumar Taura a ranar 15 ga watan Oktoba, 2024.

Wannan tashin hankali yana ƙara nuna buƙatar ɗaukar matakan tsaro ga motocin dakon mai a Najeriya domin kare rayuka da dukiyoyi daga irin wannan bala’i.

By ukarofi