
Daga SANUSI MUHAMMAD a Gusau
Iyalan Marigayi Magaji Lawali, wanda ake zargin kwamandan CPG na Zamfara, Kanal Rabi’u ‘Yandoto (rtd) ne ya kashe shi, sun yaba wa kwamishinan ƴan sandan jihar, Gwamna Dauda Lawal da kuma kwamishinan Shari’a na jihar bisa jajircewa da suka yi wajen ganin an yi wa mahaifinsu adalci.
Alhaji Nura Lawali Magaji ‘Yandoto ne ya bayyana hakan a wata tattaunawa da ya yi da Blueprint Manhaja jim-kaɗan bayan kammala zaman kotu a Gusau, a ranar Laraba.
“Mun tashi da mummunan lamari a gidanmu a lokacin da aka kashe mana mahaifi, Magaji Lauwali ‘Yandoto, wanda ya bar ƴaƴa 23, kuma ginshiƙin al’ummarmu, wanda ƙwararren jami’in soja ne kuma tsohon kwamandan rundunar kare al’umma ta jihar Zamfara (CPG), Kanal Rabiu ‘Yandoto ne ya kashe shi a watanni baya.”
Ya ce, “A yanzu haka Rabi’u ‘Yandoto yana tsare, kuma muna da yakinin za’a yi adalci.”
Ya yi kira ga hukumomi da su tabbatar wanda ya aikata laifin ya fuskanci fushin doka.
Lawali Magaji ya ƙara da cewa, “Muna yaba wa kwamishinan ƴan sanda, Ma’aikatar Shari’a, da Alƙalan Zamfara bisa jajircewarsu wajen tabbatar da doka da adalci.”
Ya bayyana Gwamna Dauda Lawal a matsayin shugaba na gari wanda ya himmatu wajen kawo ƙarshen rashin tsaro da Zamfara ke fama da ita sama da shekaru goma.
A wata hira da Blueprint Manhaja, shugaban ƙungiyar da ke kula da masu ƙaramin ƙarfi a jihar, Malam Murtala Ibrahim Zakoli ya bayyana cewa ƙungiyar za ta ci gaba da bibiyar lamarin har sai an yi adalci ga iyalan mamacin.
Idan za a iya tunawa, a watan Agustan shekarar nan ne wata tawagar jami’an tsaron al’ummar jihar ta CPG, ta kama Marigayi Magaji Lawali, wanda abokin siyasar Sanata Kabiru Garba Marafa ne a gidansa dake garin ‘Yandoto a ƙaramar Hukumar Tsafe, kuma ya mutu a hannunsu washe gari.
