
Daga BELLO A. BABAJI
Rundunar Sojoji ta sanar da ranar binne gawar marigayi Shugaban Sojojin ƙasa (COAS), Lt Janar Taoreed Lagbaja.
Lagbaja, ya mutu ne ya na da shekaru 56 bayan fama da wani rashin lafiya.
A ranar 19 ga watan Yunin 2023 ne, Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya naɗa marigayin a matsayin COAS.
Tuni Shugaba Tinubu ya umarci a yi jana’izarsa a mataki na ƙasa.
Wan marigayin, Moshood Lagbaja, a Osogbo, babban birnin Jihar Osun, ya bayyana cewa, za a binne mamacin ne a ranar Juma’a a Abuja.
Ya ce, rundunar bata ba su gawar mamacin ba, amma sun tabbatar musu da cewa za a yi jana’izarsa cikin karramawa.
Cikin wani saƙo da Kakakin sojoji, Onyema Nwachukwu ya wallafa a shafin rundunar na X, ya ce za a fara taron jana’izar ne a ranar Alhamis tare da rara waƙe-waƙe a filin fareti na ‘Mogadishu Cantonment’ inda a ranar Juma’a kuma sai kammala a Cibiyar Kiristoci ta Ƙasa da ke ‘Central Business District’.
