Daga ABDULLAHI MUHAMMAD a Katsina
Gwamnatin Jihar Katsina ta mayar da mutane tara da rundunar sojoji na 17 suka ceto a dajin Kaduna ga iyalan su.
Mutanen sun haɗa da maza bakwai da mata biyu da tuni sun koma ga muhallin su.
Mataimakin na musamman akan waɗanda harin yan bindiga ya shafa da yan gudun hijira Alhaji Sa’idu Ibrahim Ɗanja kogunan Jibiya ya bayyanawa manema labarai haka a Katsina.
Yace gwamnatin Katsina kuma ta bawa kowannen su Naira dubu 100.000 domin su sami wata sana’ar da zasu yi.
Haka kuma kogunan Jibiya ya sanar da cewa gwamnatin jihar ta tallafawa waɗanda hare haren ‘yan bindiga ya shafa a ƙananan hukumomin Musawa da Ɗandume da kuɗi Naira miliyan 20.
Alhaji Sa’idu Ibrahim ya yaba da irin namijin ƙoƙarin da jami’an tsaro ke nunawa wajen dawo da zaman lafiya a jihar.
“Babu shakka zaman lafiya ya fara dawowa a mafi yawan ƙananan hukumomin da ‘yan bindiga suka addaba sai dai ɗan abinda da ba a rasa ba”koguna yace .
Ya kuma jinjina ga Gwamna Dikko Raɗɗa akan irin yadda yake ba harkar tsaro mahimmanci tun hawan shi mulkin jihar.
