‘
Daga UMAR GARBA a Katsina
Wata dabar ‘yan bindiga ɗauke da muggan makamai sun kai farmaki a ƙauyukan Mai Ɗoriya da kuma Ɗan Alhaji a ƙaramar hukumar Batsari dake jihar Katsina.
‘Yan bindingar sun kashe mutane biyu tare da yin garkuwa da wasu fiye da 30 a ƙauyukan biyu.
Majiyarmmu ta bayyana cewa, an yi garkuwa da mutane 25 da suka haɗa da mata da ƙananan yara a unguwar Ɗan-Alhaji, yayin da wasu da dama suka samu raunukan harbin bindinga.
A ƙauyen Maiɗoriya, ‘yan bindigar sun yi wa mutane biyu yankan rago tare da yin garkuwa da wasu mutum bakwai da suka haɗa da mata shida da kuma namiji ɗaya tare da jikkata wasu 12.
Lamarin dai na zuwa ne ƙasa da mako guda bayan da wasu ‘yan bindiga suka yi garkuwa da mutane da dama a garin Gaje da ke maƙwabtaka da ƙauyen.
Ƙaramar hukumar Batsari na daga cikin ƙananan hukumonin da ke fuskantar hare haren ‘yan bindinga a jihar Katsina duk da ƙoƙarin da hukumomi ke cewa suna yi don shawo kan matsalar.
Har zuwa haɗa wannan rahoton rundunar ‘yan sanda ta jihar bata yi ƙarin bayani ba game da lamarin.
