Yadda ɗan majalisa ya baje miliyoyin nairori a gidansa duk da halin matsi da al’umma ke ciki

Spread the love

Daga BELLO A. BABAJI

Wani ɗan Majalisar Wakilai daga Jihar Kano mai suna Aliyu Sani Madaki ya janyo cecekuce acikin al’umma bayan da aka gansa cikin hotuna da bidiyo a ɗakinsa da wasu maƙudan kuɗaɗe a gabansa.

Madaki, wanda ɗan jami’yyar NNPP ne da ke wakiltar mazaɓar Dala, an gan shi tare da wasu mutum biyu su na ƙirga kuɗaɗen waɗanda ana hasashen ba za su yi ƙasa da Naira miliyan 500 ba.

Al’umma da dama musamman a halin matsin rayuwa da ake fama da shi a Nijeriya na mamakin yadda ɗan majalisar ya mallaki tsabar kuɗi irin haka a daidai lokacin da bankuna ba sa bada sama da Naira 50,000 ga masu asusu.

Sun koka game da yadda ya mallake su da kuma wani banki ne ke da alhakin ba shi su.

Mutane sun yi ta tsokaci game da hakan musamman a kafafen sada zumunta inda wasu na ganin lamarin a matsayin kuɗaɗe ne da aka sata kuma ake bayyana wa al’ummar da aka rufe musu baki.

Wasu ko ganin hakan su ke a matsayin bai wa mutane kifi a madadin nuna musu yadda za su kama ta hanyar samar musu da ayyukan yi da dogaro da kawunansu.

By Babaji