Daga AISHA ASAS
Daɗaɗɗen abu ne yekuwa da jan kunne da ake yi kan ƙayyade iyali, wanda ake danganta shi da rashin iya ba wa yara ingantacciyar tarbiyya da ababen more rayuwa idan suka yi yawa.
Shirin ƙayyade iyali ya sha suka musamman ma a Arewacin Nijeriya, inda da yawa suke kafirta wanda ya zo masu da shirin, har suke ganin su a matsayin ‘yan kwangilar yahudu da nasara.
Da wannan ne da yawa daga masu rajin kare haƙƙin ƙananan yara da hukumomin lafiya suka bayyana cewa, Arewa ba za ta taɓa karɓar tsarin ƙayyade iyali ba, duba da irin yadda ake yawaita ƙyanƙayshe yara da lokuta da dama ake tura wa almajiranci.
Saidai abin mamaki shi ne, bincike ya tabbatar da samun raguwar haihuwa a tsakanin shekarar 2023 zuwa 2024. Abin tambayar shin sun ɗauki huɗuwar ta yahudu da nasara ce? Ko kuwa wani abin ne na daban.
Ku gyara zama, domin shafin Iyali na jaridar Blueprint Manhaja zai warware maku biri har wutsiya.
Yawan haihuwa a Najeriya ya ragu a cikin ‘yan shekarun nan, inda a shekarar 2023 zuwa 2024 ƙididdigar yawan jama’a da ta kiwon lafiya ta Najeriya, NDHS, sun nuna cewa, a halin yanzu mata sun samu ƙarancin haihuwa, inda suka koma a layin tsaka-tsaka, don haka ake haihuwar yara 4.8, wanda ya ragu daga 6.3 da ke a shekarar 2008.
A rahoton da NDHS ta saki, wanda Kamfanin Dillancin Labarai na Najeriya ya wallafa ranar Laraba, a Abuja, ya nuna irin ci gaban da aka samu wajen wayar da kan kayyaɗe iyali duk da cewa akwai bambanci tsakanin ci gaban da aka samu a birane da kuma na karkara.
Kuma shi wannan binciken da aka yi, an gudanar da shi ne a tsakanin mata masu shekaru 15 zuwa 49.
Binciken ya kuma nuna yadda yawan haihuwa ya fi yawaita a yankunan karkara fiye da na birane, inda matan karkara ke da tsakanin yara 5.6, yayin da matan birane ke da yara 3.9 a matsayin matsakaici.
Hakan na nufin alƙaluman sun nuna buƙatar faɗaɗa ayyukan kiwon lafiyar haihuwa a yankunan karkara.
Rahoton ya kuma nuna bambancin da ke akwai a yawan haihuwa a faɗin ƙasar.
Haka zalika, binciken ya nuna cewa yankin Arewa maso gabas ya fi kowane yanki yawan yara da kashi 6.1, inda Arewa maso yamma ke biye da kashi 5.9.
Yankin Kudu maso Kudu ne ke da mafi ƙarancin yawan haihuwa a kashi 3.3, wanda ke nuna yanayin al’umma daban-daban a cikin ƙasar, kamar yadda rahoton ya ambata.
Bayaga haka, rahoton ya kuma nuna damuwa kan yawaitar haihuwa a tsakanin matasa, inda ya bayyana shi a matsayin abin damuwa, duba da yadda matasan Najeriya ke ci gaba da fuskantar kasadar ɗaukar ko yin ciki da wuri, a cewar dai na rahoton.
A ɓangare ɗaya, Hukumar NDHS ta bayyana cewa, kashi 15 cikin 100 na mata masu shekaru 15 zuwa 19 na ɗauke da juna biyu, inda kashi 11 cikin 100 sun riga sun haihu.
Za mu ci gaba mako mai zuwa, da yardar Allah.
