NAPTIP ta ceto mata 25 a Kano da Jigawa da ake shirin safararsu zuwa Saudiyya

Spread the love

Daga MAHDI MUSA MUHAMMAD

Hukumar Yaƙi da Fataucin Mutane ta ƙasa (NAPTIP) ta ceto mata 25 daga hannun wata ƙungiyar safarar mutane.

A cikin wata sanarwa da kakakin hukumar ta NAPTIP Vincent Adekoye ya fitar, ya ce matan da ake zargin an yi musu fyaɗe suna kan hanyarsu ta zuwa ƙasar Saudiyya kafin a ƙwato su a Abuja da ke Nijeriya.

An tsince waɗanda abin ya rutsa da su ne a gaban wani fitaccen otel da ke unguwar highbrow na Wuse II, Abuja, inda suka taru suna jiran mai safarar su.

A yayin da ake yi musu tambayoyi, waɗanda lamarin ya rutsa da su, waɗanda shekarunsu ya haura 17 zuwa 43, sun yi iƙirarin cewa wasu mutane ne suka ɗauke su aiki daga jihohin Kano, Jigawa, da Katsina tare da yin alƙawarin kai su ƙasar Saudiyya domin yin aikatau.

“Wasu mutane sun zo ƙauyenmu ne suka shaida wa iyayena cewa za su taimaka mana mu fita waje don yin aikatau a Saudiyya, sun ba mu tabbacin cewa aikin da za my yi zai kawo mana kuɗi sosai, kuma za mu iya zuwa mu kula da iyayenmu a gida.

“Sun buƙaci mu zo mu jira su a nan domin su ba mu takardar tafiye-tafiye da kuma umarnin da suka dace kan yadda za mu je, ba su ba mu wani takarda ba, kamar fasfo na ƙasa da ƙasa da biza, kuma mun damu da cewa babu ɗaya daga cikin mutanen da ya zo ya same mu kamar yadda suka yi alƙawari,” inji ɗaya daga cikin waɗanda abin ya shafa.

An ruwaito cewa, wasu da dama daga cikin waɗanda abin ya shafa sun amsa cewa zuwansu Abuja kenan a karon farko, kuma sun maƙale.

Darakta Janar na hukumar ta NAPTIP, Binta Bello, wadda ta koka da yadda masu safarar ke yi, ta yi gargaɗin cewa yanzu haka wasu ƙungiyoyin masu safarar mutane na amfani da Abuja a matsayin cibiyar hada-hadar safara.

By ukarofi