Har yanzu kashi 67 na fursunonin Nijeriya suna jiran shari’a – Tunji-Ojo

Spread the love

Daga MAHDI MUSA MUHAMMAD

Kusan kashi biyu bisa uku na fursunonin da ake tsare da su a gidajen yarin Nijeriya na ci gaba da jiran shari’a, Ministan Harkokin Cikin Gida Olubunmi Tunji-Ojo ya bayyana, yana mai jaddada buƙatar yin garambawul da kuma haɗa ƙarfi da ƙarfe tsakanin gwamnatocin tarayya da na jihohi.

Da yake magana kan harkokin siyasa a yau, wani shiri na yau da kullum da aka watsa a gidan Talabijin na Channels a ranar Alhamis, Tunji-Ojo ya ce kusan kashi 67 na fursunoni a faɗin ƙasar ba a yanke musu hukunci ba, yayin da kusan kashi 72 na ɗaukacin fursunonin masu laifuka ne daga jihohi.

Wannan lamarin, inji shi, ya ɗora wa Gwamnatin Tarayya nauyi, wadda ke tafiyar da mafi yawan gidajen yarin

“Za mu iya samar da haɗin kai… jihohin da ke son samun nasu gidajen yarin suna da damar samun su.

“Amma kuma dole ne mu fahimci cewa kusan kashi 72 na fursunoninmu masu laifi daga jihohi ne kuma kusan kashi 67 na jiran shari’a,” inji Tunji-Ojo.

“Kashi biyu bisa uku masu laifin jihohi ne, amma gwamnatin tarayya ce ke ɗaukar nauyin su yanzu.”

Ministan ya jaddada cewa gwamnatin Tinubu ta mayar da hankali ne wajen lalubo bakin zaren maimakon zargi.

Ya ƙara da cewa, “Kamar yadda mai girma shugaban ƙasa ya saba cewa, ‘An zaɓe mu ne don samar da sakamako, ba wai don neman uzuri ba.”

Tunji-Ojo ya bayyana cewa, a watan Yuli, gwamnatin tarayya ta saki fursunoni 4,550 a wani shiri na rage cunkoso a faɗin ƙasar. An saki mutanen da ake tsare da su kan ƙananan laifuffukan da za a iya bayar da belinsu da kuma waɗanda suka shafe tsawon lokaci a tsare ba tare da an gurfanar da su a gaban kotu ba.

Ya jaddada cewa tun lokacin da shugaban ƙasa Bola Tinubu ya hau kan karagar mulki a shekarar 2023, an samar da muhimman kayayyakin more rayuwa domin inganta yanayin cibiyoyin gyaran hali a faɗin ƙasar nan.

“Wannan gwamnatin ta yi abubuwa da yawa a cikin shekaru biyu da suka gabata ta fuskar samar da kayan aiki wajen gyara cibiyoyin gyaran mu,” inji shi.

Kalaman na ministan na zuwa ne biyo bayan wani harin da aka kai a gidan yari a gidan yari da ke Keffi a jihar Nasarawa, inda fursunoni 16 suka yi galaba a kan jami’an tsaro tare da tserewa a farkon wannan watan.

Daga baya an sake kama wasu da suka tsere, amma lamarin ya ƙara dagula lamurra a gidajen yari a Nijeriya a shekarun baya.

An daɗe ana alaƙanta cunkoson gidajen yari, ɗaurin da ake yi kafin shari’a, da rashin isassun kayan aiki a matsayin manyan abubuwan da ke kawo cikas ga tsarin gidajen yarin Nijeriya, lamarin da ya jawo kiraye-kirayen a yi garambawul ga majalisar dokoki da gudanarwa.

By ukarofi