Daga RABIU SANUSI a Kano
Gwamnatin Jihar Kano ta buƙaci hukumar Shari’a ta jihar Kano da ta ruɓanya ƙoƙarinta wajen shirya wa jami’anta bita akai-akai domin ƙara musu sani ta yadda za su ƙara samun ƙwarewa akan ayyukan hukumar, don ƙara ciyar da addinin Musulunci da ma al’umma gaba.
Mai bai wa gwamnan Kano shawara akan harkokin Addinai Sheikh Usamatu Salga, ne ya bayyana hakan a wajen taron ƙarawa sakatarorin hukumar Shari’a na ƙananan hukumomin Kano 44, sani akan ayyukan su, na kwanaki biyu Asabar da Lahadi, da ke gudana a Dutsen jihar Jigawa.
Gwamnatin Kano ce dai ta shirya taron ƙarawa juna sanin, mai taken “Two Days Retreat on Capacity Building” ta ofishin hukumar Shari’a ta jihar Kano ƙarƙashin jagorancin shugaban ta Sheikh Abbas Abubakar Daneji.
Sheikh Usamatu Salga, ya kuma buƙaci dukkanin jami’an gwamnatin Kano da su rinƙa bai wa hukumar Shari’a ta jihar Kano, haɗin kan da ya kamata ta yadda za su ƙara samun dama wajen gudanar da ayyukansu cikin nasara.
Da yake nasa jawabin a yayin taron, shugaban hukumar Shari’a ta jihar Kano, Sheikh Abbas Abubakar Daneji, ya ce an shirya taron ƙarawa juna sanin ne bisa yadda suka lura da raunin sakatarorin hukumar na ƙananan hukumomin Kano 44, wajen gudanar da aiki, a don haka ne aka shirya musu bitar don ƙara musu sani ta yadda za su rinƙa gudanar da aikinsu yadda ya kamata.
Tunda farko, da yake jawabin maraba a yayin taron, Kwamishina na biyu a hukumar Shari’a ta jihar Kano, Sheikh Ali ɗanAbba, ya buƙaci sakatarori da dukkanin shugabannin hukumar na ƙananan hukumomin jihar 44, da su ƙara haɗa kan su tare da kawar da dukkanin abinda zai iya kawo bambanci.
Dakta Bala Muhammad, Malami ne a sashen koyar da aikin Jarida a Jami’ar Bayero ta Kano, ya gabatar da maƙala a yayin taron akan Riƙe Sirrin Gwamnati da ofis da kuma amfanin yin hakan ko akasin haka, har ma ya shawarci dukkanin jami’an gwamnati da su kasance masu riƙe sirrin wurin da suke aiki, don gujewa fuskantar matsala.
Taron, ya samu halartar al’umma da dama, kuma ciki har da Kwamishinan harkokin Addinai na jihar Kano Sheikh Ahmad Tajjani Auwal, da Kwamishina na ɗaya a hukumar Shari’a ta jihar Kano Gwani Hadi ɗahiru Yakasai, da daraktocin hukumar, da sakatarori da ma wasu shugabannin hukumar na ƙananan hukumomin Kano, da dai sauransu.
