Kungiyar Likitoci ta bai wa Gwamnan Kaduna wa’adin kwanaki 12 ya biya su haƙƙoƙinsu ko su tsunduma yajin aiki

Spread the love

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja 

Kungiyar likitocin ARD dake Babban Asibitin koyarwa na Barau Dikko a jihar Kaduna ta bai wa gwamnati wa’adin kwanaki 12 domin ta biya buƙatunsu ko ta ci gaba da yajin aikin da ta dakatar kwanakin baya.

Shugaban ƙungiyar reshen jihar Kaduna Josiah Yakubu wanda ya sanar da haka wa Kamfanin Dillancin Labaran Nijeriya NAN ya ce ƙungiyar ta buƙaci gwamnati ta fara biyan likitoci da tsarin CONMESS 2024 wanda aka gyara tare da biyan su albashinsu na watanni biyu da suka gabata da ba a biya ba.

Yakubu ya ce ƙungiyar ta amince ta bada wa’adin kwanaki 12 ne wanda ya fara daga ranar 18 ga Agusta a zaman da ta yi.

Ya ce har yanzu fannin kiwon lafiya jihar na fama da matsalar yawan ficewar likitoci daga jihar zuwa asibitocin Gwamnatin Tarayya da asibitocin Gwamnatin dake kusa da su saboda samun albashin mai tsoka wanda hakan ke kara zurfin matsalar ƙarancin ma’aikata da aiki ke neman fin ƙarfinsu.

Yakubu ya miƙa godiyarsa ga gwamnatin jihar kan ƙoƙarin da ta yi wajen tattauna hanyoyin biyan buƙatunsu.

Ya ce har yanzu ƙungiyar ta ji shiru kan biyan buƙatunta da gwamanti ta yi alƙawarin biya daga lokacin zuwa watanni biyu duk da sa hannun da gwamnati ta yi tare da su kan takarda yarjejeniyar biyan buƙatunsu.

ƙungiyar ta tabbatar cewa rashin biyan buƙatunsu nan da ƙarshen wannan wata zai za ƙungiyar ta ci gaba da yajin aikin da ta dakatar ranar 5 ga Agusta.

Yakubu ya yi kira ga likitoci da su ci gaba da gudanar da ayyukkan su yadda ya kamata domin bai wa gwamnati samar biyan su da tsarin CONMESS ta 2024 daga wannan wata na Agusta da sauran buƙatunsu a tsakanin lokacin da suka bada.

Sauran buƙatun sun haɗa da ɗaukar likitocin dake samun horo aiki tare da biyan su albashi mai tsoka domin tabbatar da sun tsaya domin inganta fannin lafiyar jihar.

Ya ce ƙungiyar za ta ci gaba da haɗa hannu da ƙungiyar NMA, NARD da sauran masu ruwa da tsaki na fannin lafiya domin tabbatar da gwamnati ta biya buƙatunsu.

By ukarofi