Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja
Hukumar Kwastom ta Nijeriya, shiyyar Katsina, ta cafke miyagun ƙwayoyi da darajarsu ta kai Naira miliyan 690 a lokacin sintiri a iyakokin jihar.
Kwanturola Idriss Abba-Aji, kwamandan hukumar a Katsina, ya bayyana wa manema labarai cewa jami’an kwastam sun gano kartani 14 na tramadol da darajarsu ta kai kimanin Naira miliyan 650, tare da ƙwayoyin Fragbaline da suka kai kusan Naira miliyan 28, da kuma tabar wiwi (cannabis satiɓa) da aka kiyasta darajarsu a kan Naira miliyan 15.
Wannan kamun, inji shi, ya kasance mafi girma a tarihin shiyyar.
Ya ce masu safarar miyagun ƙwayoyin suna ɓoye su ne cikin motoci da ba a yi zaton haka ba.
“Wasu lokutan ma har a cikin mota da alama kamar na manyan mutane suke ɓoyewa. Amma dukkan abin dole sai an tsayar, an bincika, sannan ake gano su,” inji shi.
Hukumar ta ce an kama mutum ɗaya da ke tuƙa ɗaya daga cikin motocin, amma daga bisani aka ba shi beli na wucin gadi.
Kwanturola Abba-Aji ya kuma jaddada cewa yawancin matsalolin tsaro musamman ta’addanci da fashi a arewacin ƙasar na da alaƙa da shan miyagun ƙwayoyi. Ya ce hukumar za ta ci gaba da tsaurara matakan tsaro tare da kira ga jama’a da su taimaka wajen daƙile safarar miyagun ƙwayoyi a iyakokin jihar Katsina.
