Babu yankin da ‘yan ta’adda ke iko a Jihar Neja yanzu – Bago

Spread the love

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja 

Gwamnan Jihar Neja, Mohammed Bago, ya bayyana cewa babu wani yanki a jihar da ‘yan ta’adda ke iko a kansa a halin yanzu, yayin da ya tabbatar da cewa gwamnatin jihar tare da ta tarayya na aiki tuƙuru wajen tabbatar da tsaro da kuma daƙile ayyukan yan ta’adda.

Bago ya bayyana haka ne a wata tattaunawa da aka yi da shi a tashar Arise TV a ranar Litinin, inda ya ce shekaru da dama na barin dazuzzuka da “ba tare da shigowar gwamnati ba” ya ba ’yan ta’adda damar kafa maɓoya, amma yanzu gwamnati ta fatattake su gaba ɗaya.

“Mun ci nasara sosai. Mutane sun koma gidajensu, babu wani yanki da ’yan ta’adda ke iko a kai a Neja. A Shiroro da Munya mun gudanar da zaɓe cikin kwanciyar hankali, mutane suna gudanar da rayuwarsu kamar yadda aka saba,” inji Gwamna Bago.

Gwamnan ya bayyana cewa a halin yanzu Jihar Neja tare da UNDP na gina gidaje sama da 350 don sake tsugunar da mutanen da suka rasa muhallansu.

By ukarofi